Harin Garkida: Muna kallon jiragen sojin saman Najeriya a kan mu lokacin da 'yan Boko Haram suka kawo mana hari

Harin Garkida: Muna kallon jiragen sojin saman Najeriya a kan mu lokacin da 'yan Boko Haram suka kawo mana hari

- Wasu mazauna kauyen Garkida da ke karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa sun nuna rashin jin dadinsu ta yadda sojoji suka ki taimaka musu

- Mazauna yankin sun bayyana cewa, sun kai wa sojojin Chibok korafin cewa ‘yan ta’adda na tunkaro garinsu kuma an sanar da rundunar sojin sama

- Kamar yadda suka bayyana, ana tsaka da kai musu harin sun hango jiragen yaki na ta shawagi, amma ko harbi daya basu yi wa ‘yan ta’addan ba balle bam

Wasu mazauna Garkida da ke karamar hukumar Gombi ta jihar Adamawa sun zargi rundunaar sojin saman Najeriya da kin daukar mataki yayin da mayakan Boko Haram suka kai musu hari a makon da ya gabata.

Mazauna kauyen sun sanar da jaridar The Cable cewa, hukumomin NAF din sun san ana kai musu hari amma sai suka hangi jiragen yakin sojin na kai kawo a sararin samaniya.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, “Mun hango mayakan Boko Haram din a lokacin da suka iso Korongilum kuma da gaggawa muka sanar da bataliyar soji mafi kusa da mu wacce ta ke Chibok. Daga nan sai suka kira sojin sama don bamu taimako. Mayakan Boko Haram din suna cikin garinmu amma sai muka dinga ganin jiragen yakin na yawo a sama. ‘Yan ta’addan sun dau sa’o’i uku suna mummunan aikinsu amma ko harbi daya basu samu daga sojin ba. Bayan sun kammala ne suka wuce a tawagarsu wacce ta kunshi motoci 17.”

KU KARANTA: Coronavirus: An haramta ci da sayar da kowanne irin nau'i na namun daji a kasar China

Wani mazaunin yankin ya ce; “yayin da muka gudu cikin tsaunika don buya, mun ga jiragen yaki na yawo a sama amma babu abinda suka yi wa ‘yan ta’addan.”

Kamar yadda wani mazaunin yankin ya sanar, “har mun fara tambayar kanmu ko dai mayakan Boko Haram din suna da jiragen kansu ne? Ko kuma sojin saman basu ganin ‘yan ta’addan ne. Muna bukatar taimako amma sun hana mu.”

Wani babban jami’in sojin wanda ya sanar da jaridar The Cable aukuwar lamarin, ya ce sojojin sun kasa banbance ‘yan ta’addan da jama’ar garin ne.

Ya ce sojojin kasa da ke yankin basu da kayan aiki ne. Motar yaki daya kacal ce a tare da su kuma mayakan Boko Haram din sun fi su yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel