Wani mutum ya soke abokinsa har lahira kan bashin N1,200

Wani mutum ya soke abokinsa har lahira kan bashin N1,200

Rahotanni sun kawo cewa an kama wani mutum mai shekara 42, Emmanuel Osiben kan zargin soke abokinsa mai shekara 38, Femi har lahira yayinda ya ke kokarin karban bashin naira 1,200 da ya ke binsa.

Sai dai Osiben wanda ya mallaki wani cibiyar kallo a yankin Ijora-Badia da ke Lagas, ya yi zargin cewa marigayin ne ya fara kai masa hari da kwalba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a yanzu haka ana nan a tsare mai laifin a sashin binciken masu laifi, da ke Panti, Yaba kan aikata kisan kai.

An tattaro cewa wasu makwabta ne suka kama mai laifin sannan daga misani suka mika shi ga yan sanda a yankin Badia, jahar Lagas.

Wani mutum ya soke abokinsa har lahira kan bashin N1,200
Wani mutum ya soke abokinsa har lahira kan bashin N1,200
Asali: Twitter

Osiben yayinda ya ke fallasa ga yan sanda, ya amsa cewa ya tunkari marigayin, wanda ya yi ikirarin cewa yana binsa N,1200.

Ya ce: “Lamarin ya afku ne a ranar 13 ga watan Fabrairun 202 a Ijora Badia. Na je karban bashin N1,200 da nake bin Femi. Amma sai ya fara hayaniya dani sai muka kaure da fada.

"Wasu dattawa da ke wajen sun raba mu sannan na tafi gidana don yin abincin rana.

“Ina a gidana ina fere doya lokacin da Femi ya shigo sannan ya fasa kwalba a kaina. Sai na dauki wuka da nake fere doya dashi na soke shi a wuya.

“Dukkaninmu muna zubar jini lokacin da wadanda suka raba mu da baya suka iso. Sai aka yi gaggawan kai mu asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa. Makwabta suka kama ni suka mika ni ga yan sanda.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kashe yan fashi 5 a musayar wuta da suka yi a Katsina

“Na yi danasanin abunda ya faru domin marigayin abokina ne. Ba don haka ba, mai zai san a ranta masa kudi?"

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jahar Lagas, Bala Elkana ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton domin an ce yana cikin wata ganawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel