PDP ta bukaci kotun koli ta sake nazari game da hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa na 2019

PDP ta bukaci kotun koli ta sake nazari game da hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa na 2019

Uwar jam’iyyar PDP ta yi kira ga kotun kolin Najeriya ta sake duba shari’ar zaben shugaban kasa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da dan takararta Atiku Abubakar domin ta sake gudanar nazari game da hukuncin.

Baya ga wannan, haka zalika PDP ta bakin mai magana da yawunta, Kola Ologbondiyan ta nemo kotun koli ta sake duba hukunce hukuncen da ta yanke a shari’un zabukan gwamnonin jahohin Osun, Kano, Kaduna da Katsina, kuma ta sake nazarin hukunce hukuncen.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta shawarci PDP ta koma noman shinkafa tunda ba ta da aikin yi

A watan Oktobar da ta wuce ne kotun koli ta yi fatali da karar PDP inda take kalubalantar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a kan Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na watan Feburairun shekarar 2019.

Sai dai Kola ya ce: “PDP ta yanke shawarar sake tunkarar kotun koli game da batun ne sakamakon yunkurin APC na raba kotun da yi ma tsarin sharia katsalandan don bukatar kansu, yan Najeriya suna sane da cewa APC ta zubar da jini biyo bayan rasa jahohin Bayelsa da Zamfara ta hanyar sahihin hukunci.

“Don haka basu kaunar fahimtar hikimar dake cikin hukunce hukunce, kuma sun kuduri aniyar lalata dimukradiyyar da muka wahala wajen ginata, musamman ma bangaren sharia, gwamnatin APC na jagorantar yaki da doka da kundin tsarin mulki.” Inji shi.

Daga karshe Kola ya ce a matsayinsuna babbar jam’iyyar adawa ba za su kama hannu su zura idanu yayin da makiyan dimukradiyya wanda basu bayar da gudunmuwar komai ba wajen ginata, su rushe ta ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta yini guda jahar Ondo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jahar ta kammala a karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu SAN.

Gwamna Rotimi da kansa tare da manyan jami’an gwamnatinsa ne za su tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yan tawagarsa, inda shugaban zai kaddamar da wani katafaren gadar sama da cibiyar masana’antu a garin Ore, na karamar hukumar Odigbo.

Ana sa ran jagoran jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na daga cikin wadanda zasu raka shugaba Buhari zuwa Ondo, kafatanin gwamnonin jahohin yarbawa 6, ministoci daga yankun Yarbawa da kuma yan majalisu daga jahar Ondo duk zasu halarci taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel