Boko Haram: Zulum ya yi wa 'yan Najeriya godiya saboda taya 'yan Borno azumi

Boko Haram: Zulum ya yi wa 'yan Najeriya godiya saboda taya 'yan Borno azumi

- Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya mika sakon godiya ta musamman ga 'yan Najeriya da suka yi azumi a ranar Litini tare da 'yan jiharsa

- Mutanen jihar ta Borno sun yi azumin na musamman ne a ranar Litinin domin fatan Allah ya kawo karshen kallubalen ta'addanci da ya adabi jihar

- Gwamna Zulum ya ce tsoron Allah ne kawai sai saka mutane yin azumin kuma ya mika godiyarsa ga dukkan 'yan Najeriya na Borno da wasu jihohin da suka yi azumin

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a cikin wata sakon da ya aike wa 'yan Najariya a daren jiya Litinin ya aike da sakon godiya ga al'ummar Najeriya na gida da waje da suka yi azumi tare da 'yan jiharsa da kuma addu'a domin kawo karshen ta'addancin kungiyar Boko Haram.

DUBA WANNAN: Mu na alfahari da almajiranci, bai kamata a hana ba - Adamu Garba

Gwamnan cikin sakon da ya aike wa 'yan kasar mai taken 'Za mu yi fada da su, za mu yi azumi kuma za mu yi addu'a' ya ware rana guda domin yin azumi da addu'a domin kawo karshen matsalar ta'addanci da ya addabi jihar.

An tattaro cewa a sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce: "Ina mika godiya ta ga sauran 'yan Najeriya da ke jiha ta da wadanda ke wajen Borno saboda yin azumi yau. "Na san cewa anyi wannan ibada mai muhimmanci ne saboda Allah.

"Ina mika godiya ta ga 'yan Najeriya saboda addu'ar da suka yi a yau," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel