A karon farko 'yan fim din Hausa dana kudancin Najeriya za su fitar da wani shahararren fim da suka yi tare

A karon farko 'yan fim din Hausa dana kudancin Najeriya za su fitar da wani shahararren fim da suka yi tare

- Wani shahararren fim da ya hada manyan jarumai daga Kannywood da Nollywood zai fito a 2020

- Fim din mai suna 'The Right Choice' ya hada jarumai irinsu Ali Nuhu, Abba El-Mustapha kuma jarumi Ali Nuhu ne ya bada umarni

- Furodusoshi biyu Bashir MaiShadda da Kabiru Jammaje ne mamallakan fim din kuma sun kashe a kalla naira miliyan talatin da biyar

Fim daga masana'antar Kannywood mai suna 'The Right Choice' ya kunshi jarumai daga Kannywood da kuma Nollywood. Babu shakka yana daya daga cikin manyan fina-finai a 2020.

Furodusoshin babban fim din mutane biyu ne; Bashir Maishadda da kuma Kabiru Jammaje. Sun kashe a kalla naira miliyan 35 don samun gawurtattun 'yan wasa.

A karon farko 'yan fim din Hausa dana kudancin Najeriya za su fitar da wani shahararren fim da suka yi tare
A karon farko 'yan fim din Hausa dana kudancin Najeriya za su fitar da wani shahararren fim da suka yi tare
Asali: Facebook

'Yan wasan sun hada da: Sani Mu'azu, Segun Arinze, Sola Sobowale, Nancy E. Isime, Enyinna Nwigwe, Ali Nuhu, Abba El-Mustapha, Asabe Madaki da sauransu.

Shahararren fim din ya samu bada umarni ne daga Ali Nuhu.

A yayin zantawa da jaridar Daily Trust, Maishadda ya ce wannan fim din zai zama mafi shahara a masa'antar.

KU KARANTA: Za a gabatar da kudurin da za a dinga bawa dalibai aiki da zarar sun kammala bautar kasa

"The Right Choice shine fim din Kannywood na farko da ya tattara manyan jaruman Nollywood da Kannywood," ya ce.

Ya kara da cewa yanayin tsarin labarin da hada shi tare da kasafin kudin da ya ci duk ba irin kowanne fim bane.

"Tun daga kafa masana'antar, babu wani fim da ya ci kudi kamar wannan. Mun kawo manyan jarumai daga Nollywood sannan muka hada su da na Kannywood. Ina da tabbacin cewa duk masoyin fina-finan Hausa zai so fim din. Ina da tabbacin zamu samu riba mai matukar yawa."

Maishadda ne furodusan Mariya, Kanwar Dubarudu, Mujadala, Hafeez, Sareena, Hauwa Kulu da Wutar Kara.

Alamu na nuni da cewa wannan fim da za ayi dai shine fim mafi girma da tsada a tarihin fina-finan na Kannywood.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel