Shugaban hukumar yaki da rashawa ya lashi takobin cigaba da binciken Sarki Sunusi

Shugaban hukumar yaki da rashawa ya lashi takobin cigaba da binciken Sarki Sunusi

Shugaban hukumar yaki da rashawa da karban koken jama’a na jahar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado ya bayyana cewa hukumarsa na duba matakan da ya kamata ta dauka biyo bayan hukuncin da babbar kotun tarayya dake Kano ta yanke.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, ta ruwaito a hukuncin ya danganci rahoton da hukumar ta fitar ne a kan zargin da take ma Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II na barnatar da kudin masarauta naira biliyan 3.4 wanda Sarki ya nemi kotun ta soke shi.

KU KARANTA: Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3

Daga karshe kotun ta yanke hukunci a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta soke rahoton sakamakon rashin baiwa Sarki Sunusi daman kare kansa kamar yadda sashi na 36 na kundin tsarin mulkin Najeriya ta tanadar, kuma shi ma Muhyi ya bayyana cewa: “Hukumar ta samu sakon hukuncin kotun.

“Amma bayan mun yi nazari a kan hukuncin kotun, mun fahimci cewa Alkalin kotun, Mai Sharia O.A Egwuata bai hana cigaba da gudanar da bincike ba, ko kuma mika rahoto bayan kammala binciken wanda ya shigar da kara ba.

“Don haka a yanzu hukumar tana da zabi guda biyu, kodai ta daukaka kara saboda tana da daman daukaka kara, ko kuma ta cigaba da gudanar da bincike ta hanyar gayyatar Sarkin ya bada jawabinsa kamar yadda kotun ta bukata.” Inji shi.

Sai dai Muhyi ya ce dama dalilin da yasa hukumar ta gabatar da rahoton bincikenta shi ne saboda kokarin da wanda ake tuhuma ya yi na kawo ma binciken hukumar matsala, don haka yace hukumar za ta cigaba da duba matakin da zai fi zama a’ala a gareta tun da dai har yanzu tana binciken badakalar.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta yini guda jahar Ondo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jahar ta kammala a karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu SAN.

Gwamna Rotimi da kansa tare da manyan jami’an gwamnatinsa ne za su tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yan tawagarsa, inda shugaban zai kaddamar da wani katafaren gadar sama da cibiyar masana’antu a garin Ore, na karamar hukumar Odigbo.

Ana sa ran jagoran jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na daga cikin wadanda zasu raka shugaba Buhari zuwa Ondo, kafatanin gwamnonin jahohin yarbawa 6, ministoci daga yankun Yarbawa da kuma yan majalisu daga jahar Ondo duk zasu halarci taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel