Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3

Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3

Daga dukkan alamu, Allah Ya karbi azumin da miliyoyin al’ummar jahar Borno da ma wadanda ba yan jahar ba suka yi a ranar Litinin, 24 ga watan Feburairu, kamar yadda gwamnan jahar Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukata domin neman Allah Ya kawo zaman lafiya a jahar.

Shahararren masani dangane da kungiyar Boko Haram, Audu Bulama Bukarti ne ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa rahotanni tabbatattu sun bayyana mayakan kungiyar ta’addanci na ISWAP, wani bangare na Boko Haram sun kashe manyan jagororinsu guda uku.

KU KARANTA: An baiwa ma’aikata hutu a jahar Ondo domin karrama shugaban kasa Buhari

Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3
Azumin jama’an Borno ya fara aiki: Mayakan ISWAP sun kashe kwamandojinsu guda 3
Asali: Facebook

Daga cikin manyan kwamandojin da rahotanni suka bayyana cewa mabiyansu sun kashesu a ranar Litinin, 24 ga watan Feburairu akwai shugaban kungiyar, Idris Al-Barnawa, Abu Maryam da Abu Zainab, kwamandoji biyu da suka yi ma Shekau bore a 2016.

A cewar Bulama: “Wasu kwamandoji ne suka kashe manyan kwamandojin sakamakon rashin amincewa da suka nuna da sabbin sauye sauyen da su manyan kwamandojin suka kirkiro. Sabbin sauye sauyen sun hada da sabuwar dokar cewa yan ta’adda su daina bin Sojoji idan har sun tsere, kuma su daina kashe Sojojin da aka kama.

“Don haka kwamandojin suka ga cewa dokokin sun yiisakwa sakwa, sa’annan suka zargesu da yin sanyi game da manufofin kungiyarsu, wannan ta kai ga tayar da kayar bayan da ya yi sanadiyyar kashe jagororin uku.

“A yanzu haka sun nada Abba Shayima a matsayin sabon gwamnansu, tare da Lawan Abubakar a matsayin mataimakinsa.” Inji shi.

Bulama wanda yace daga cikin majiyoyinsa akwai wani shugaban kwamandan Civilian JTF ya bayyana cewa a watan Agustan shekarar 2018 ne mayakan ISWAP suka kashe Mamman Nur, guda daga cikin wadanda suka kafa Boko Hara zarginsa da kin biyayya ga gwamnansu, watsa jita jita da kokarin tserewa daga cikin kungiyar.

Daga karshe, Bulama ya yi hasashen idan har wannan batu ya tabbata, hakan ya tabbatar da matsalar cikin gida dake kawo rarrabuwar kai a Boko Haram da har ya rabata gida uku, sa’annan mai yiwuwa ya kara tsaurara hare haren ISWAP a kan jama’a ko kuma a kan sauran bangarorin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel