An baiwa ma’aikata hutu a jahar Ondo domin karrama shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta yini guda jahar Ondo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jahar ta kammala a karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu SAN.
Gwamna Rotimi da kansa tare da manyan jami’an gwamnatinsa ne za su tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yan tawagarsa, inda shugaban zai kaddamar da wani katafaren gadar sama da cibiyar masana’antu a garin Ore, na karamar hukumar Odigbo.
KU KARANTA: An tsaurara tsaro gabanin ziyarar da Buhari zai kai jahar Ondo ranar Talata
Ana sa ran jagoran jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na daga cikin wadanda zasu raka shugaba Buhari zuwa Ondo, kafatanin gwamnonin jahohin yarbawa 6, ministoci daga yankun Yarbawa da kuma yan majalisu daga jahar Ondo duk zasu halarci taron.
Bikin kaddamar da ayyukan na daga cikin hidindimun da za’a gudanar domin murnar cikar Gwamna Akeredolu shekaru uku a kan karagar mulki, saboda haka ne gwamnan ya sanar da ranar Talata a matsayin ranar hutu don karrama shugaban kasar.
Gwamnan yace akwai bukatar ya baiwa ma’aikata hutu domin su taru gaba daya su baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari kyakkyawar tarbar da ta kamace shi a matsayinsa na uban kasa.
Shi ma kwamishinan watsa labaru na jahar Ondo, Donald Ojogo ya bayyana cewa sun kammala dukkanin shirye shiryen baiwa shugaban kasa Buhari kyakkyawar tarba.
A wani labari kuma, hukumomin tsaro sun tsaurara matakan tsaro gabanin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa garin Ore dake cikin karamar hukumar Odigbo na jahar Ondo a ranar Talata, 25 ga watan Feburairu.
Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, CSP Femi Joseph ya bayyana cewa za’a girke jami’an Yansanda da dama domin su tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu a yayin ziyarar shugaban, don haka ya yi kira ga masu ababen hawa da matafiya da su yi hakuri da sauye sauyen da za’a samu a ranar a sanadiyyar ziyarar.
Shi ma shugaban jami’an hukumar tsaro ta NSCDC na yankin, Samson Egbebiyi ya bayyana cewa tuni sun baza jami’ansu don tabbatar da tsaron yan Najeriya a yayin ziyarar shugaban kasa Buhari.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng