Abinda yasa NSA Monguno bai halarci taron Buhari da shugabannin hukumomin tsaro ba

Abinda yasa NSA Monguno bai halarci taron Buhari da shugabannin hukumomin tsaro ba

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wani taro na musamman da shugabannin hukumomin tsaro na kasa a fadarsa da ke babban birnin tarayya (FCT), Abuja.

Taron ya samu halartar shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya; Laftanal Janar T. Y Buratai, takwaransa na sojojin sama; Air Vice Marshak Sadique Abubakar, da kuma na sojojin ruwa; Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas, da kuma shugaban rundunar sojojin Najeriya (COAS); Janar Gabriel Olonisakin.

Kazalika, taron ya samu halartar babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP); Mohammed Adamu.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ta fahimci mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaron kasa (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), bai halarci taron ba saboda yana wakiltar shugaba Buhari a wani taron kasa da kasa a kan tsaro da ake yi a Munich, kasar Jamus.

Abinda yasa NSA Monguno bai alarci taron Buhari da shugabannin hukumomin tsaro ba
Babagana Monguno
Asali: Depositphotos

Ana sa ran Monguno zai dawo gida Najeriya ranar Talata bayan ya biya ta London a kasar Ingila.

DUBA WANNAN: Abinda ya hana mu yi wa mayakan Boko Haram ruwan wuta yayin harin Garkinda - NAF

A cikin makon jiya ne jaridar Premium Times ta wallafa wata takarda da Monguno ya aike wa shugabannin hukumomin tsaro a kan su daina aiki da duk wani umarni matukar ba daga bakin shugaban kasa ya fito ba.

Monguno ya aika musu takardar ne bayan ya yi korafin cewa wasu makusanta shugaban kasa na yin amfani da mukaminsu wajen bawa shugabannin hukumomin tsaron umarni, lamarin da ya ce yana kara dagula sha'anin tsaro a cikin kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel