Yanzun-nan: Mutane 5 sun mutu yayinda zanga-zangar Sagamu ya munana
- Daruruwan mutane da suka hada da mata da yara sun mamaye unguwanni a Sagamu, jahar Ogun domin nuna fushinsu kan kisan dan kwallon kafa Kazeem Tiamiyu
- Sai dai an tattaro cewa zanga-zangar bai kare ta dadi ba inda mutane biyar ciki harda yan sanda biyu suka mutu
- An tattaro cewa yan sanda ne suka kashe Tiamiyu, wanda ya kasance dan wasan kwallon kafa a kungiyar Remo a ranar Asabar
Rahotanni sun kawo cewa mutane biyar wadanda suka hada da jami’an yan sanda biyu sun mutu bayan daruruwan masu zanga-zanga da suka hada da mata da yara sun mamaye unguwanni a Sagamu, jahar Ogun domin nuna fushinsu kan kisan dan kwallon kafa Kazeem Tiamiyu.
An tattaro cewa yan sanda ne suka kashe Tiamiyu, wanda ya kasance dan wasan kwallon kafa a kungiyar Remo a ranar Asabar.

Asali: Twitter
Yan sandan dai sun kama shi ne kan zargin cewa dan Yahoo ne.
A baya dai mun ji cewa ana ta samun mabanbantan labari a game da ‘Dan wasan kwallon kafan kungiyar Reno da aka harbe a kudancin Najeriya a cikin karshen wannan makon.
An tabbatar da cewa an harbi Tiamiyu Kazeem da bindiga a jiya. Kazeem ya kasance ya na bugawa kungiyar Remo Stars da ke jihar Ogun wasa kafin a kashe shi.
Kungiyar Remo Stars ta bayyana cewa za ta yi bakin kokarinta wajen ganin an gudanar da bincike game da mutuwar tsohon Tauraron na ta, Tiamiyu Kazeem.
Kulob din ya yi wannan bayani ne a wani gajeren jawabi da ya fitar a shafin Tuwita, inda ya tabbatar da mutuwar ‘Dan wasan, sannan ya mika ta’aziyyarsa.
KU KARANTA KUMA: APC NWC: Shugaban PGF ya yi tir da rawar Shugabancin Oshiomhole
Mun samu labari daga gidan talabijin na Channels TV cewa Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bada umarnin kama Jami’in da ya yi sanadiyyar mutuwar ‘Dan wasan.
Kawo yanzu ba a san wani ‘Dan Sanda ne ya harbi ‘Dan wasan kwallon kafan ba. A dalilin kashe shi, an yi zanga-zanga a ofishin ‘Yan Sanda da ke Garin Sagamu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng