Alkali ta yi watsi da zargin da ake yi wa Ike Ekweremadu na kin bayyana kadarorinsa
A Ranar Litinin, babban kotun tarayya da ke Garin Abuja, ta yi watsi da karar da aka kawo game da tsohon ‘Dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu.
Gwamnati ta na zargin Ike Ekweremadu da kin bayyana dukiyarsa da kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada, inda ta ce ya boye wasu gidajensa da ke kasashen ketare.
Idan ba ku manta ba a shekarar 2018, hukumar SPIP da aka wargaza a karkashin Okoi Obono-Obla ta zargi Sanatan na PDP da rashin gaskiya wajen bayyana adadin dukiyarsa.
Daga baya ofishin babban Lauyan gwamnati, AGF, ta karbe wannan karar da wasu sauran shari’ar da ake yi, ta kuma maka gurfanar da irinsu Ike Ekweremadu a gaban Alkali.
Jaridar Vanguard ta bayyana cewa da aka zauna a kotu a Yau Ranar Litinin, Alkali mai shari’a, Binta Nyako, ta yi watsi da shari’ar sakamakon yadda aka gabatar da karar.
KU KARANTA: Yadda aka dage shari'ar Gwamnatin Tarayya da Ekweremadu
Lauyan gwamnatin tarayya da ke ofishin AGF, Pius Akutah, ya shaidawa Alkali Binta Nyako cewa tsohon Lauyan da ke kula da karar ya tsere da takardun da ake aiki a kai.
Pius Akuta ya roki Alkali ta mika masa takardun karar, amma Lauyan da ke kare Sanata Ike Ekweremadu, Adegboyega Awomolo SAN ya roki ayi fatali da karar kawai.
Alkalin ta na da damar ta dakatar da shari’ar har sai nan da wani lokaci ko kuma ta yi watsi da karar. A karshe dai Binta Nyako ta zabi ta yi wurgi da karar daga teburinta.
Nyako ta yi kaca-kaca da Lauyan gwamnatin, ta ce a matsayinsa ya kamata ace ya san abin da ya kamata. Ta yi watsi da karar ta ce idan an shirya a gurfanar da sabon kara.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng