An tsaurara tsaro gabanin ziyarar da Buhari zai kai jahar Ondo ranar Talata

An tsaurara tsaro gabanin ziyarar da Buhari zai kai jahar Ondo ranar Talata

Hukumomin tsaro sun tsaurara matakan tsaro gabanin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa garin Ore dake cikin karamar hukumar Odigbo na jahar Ondo a ranar Talata, 25 ga watan Feburairu.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban kasa Buhari zai kaddamar da wani katafaren gadar sama da cibiyar masana’antu a jahar Ondo wanda gwamnan jahar Rotimi Akeredolu ya shiryasu domin murnar cikarsa shekaru 3 a karagar mulki.

KU KARANTA: Yaki da rashawa: Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 160 ga wata Mata da abokanta 3

Mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, CSP Femi Joseph ya bayyana cewa za’a girke jami’an Yansanda da dama domin su tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyoyinsu a yayin ziyarar shugaban, don haka ya yi kira ga masu ababen hawa da matafiya da su yi hakuri da sauye sauyen da za’a samu a ranar a sanadiyyar ziyarar.

Shi ma shugaban jami’an hukumar tsaro ta NSCDC na yankin, Samson Egbebiyi ya bayyana cewa tuni sun baza jami’ansu don tabbatar da tsaron yan Najeriya a yayin ziyarar shugaban kasa Buhari.

“Jami’anmu daga babban ofishinmu da kuma wadanda suke nan a shirye suke su tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman kare shugaban kasa, gwamnoni da sauran tawagarsu da zasu halarci taron.” Inji shi.

Haka zalika kwamandan hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, reshen karamar hukumar Ore, Olusegun Aladenika ya bayyana cewa a shirye jami’ansa suke don su tabbatar da wucewar ababen hawa cikin sauki ba tare da tsaiko ba.

Daga bangaren direbobi da jam’an gari kuwa, sun bayyana farin cikinsu game da kammala aikin gadar saman, wanda suka ce za ta taimaka wajen rage wahalhalun da ake sha a kan titin, sa’annan sun jinjina ma gwamnan jahar Ondo bisa cika alkawarin da ya dauka.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya musanta jita jitan da ake yayatawa a kan wai zai fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ya wankan tsarki zuwa jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC.

Mai magana da yawunsa, Lere Olayinka ne ya bayyana haka a madadin Fayose, inda yace mai zai yi da APC, jam’iyyar da ta kamu da cutar Coronavirus? Don haka yace APC ba irin jam’iyyar da mutum kamarsa zai iya shiga bane.

Wannan raddi ya biyo bayan maganar da jam’iyyar APC reshen jahar Ekiti ta yi ne, inda ta bayyana cewa Fayose ba shi da kimar da za su amsheshi a cikin jam’iyyarsu, don haka Fayose yace: “Abin dariya ne yadda jam’iyyar APC a Ekiti take karya, kuma take karyata kanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel