An kama wata mata da laifin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta a Nassarawa

An kama wata mata da laifin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta a Nassarawa

Rundunar Yansandan jahar Nassarawa ta sanar da kama wata mata yar shekara 29 mai suna Paulina Santos wanda ta hada baki da wasu miyagun mutane suka yi garkuwa da mahaifiyar kawarta.

Jaridar Punch ta ruwaito mijin kawar Paulina ma’aikaci ne a kamfanin man fetir na Najeriya, NNPC. A yayin da Yansanda suka yi holen Paulina a babban ofishinsu dake garin Lafiya, kwamishinan Yansanda Bola Longe ya yi ma manema labaru karin bayani.

KU KARANTA: Fayose ya yi fatali da batun komawarsa cikin jam’iyyar APC

An kama wata mata da laifin yin garkuwa da mahaifiyar kawarta a Nassarawa
Paulina
Asali: Facebook

Kwamishinan Longe ya ce a ranar 11 ga watan Feburairu suka kama Paulina Santos, kwararrun jami’an Yansanda daga sashin yaki da sata tare da garkuwa da mutane ne suka yi nasarar cafketa.

Babban dansandan ya ce Paulina wanda ta fito daga karamar hukumar Ogbadigbo na jahar Benuwe tana zaune ne a unguwar Azuba Bashayi, cikin karamar hukumar cigaba ta Arewacin Lafia na jahar Nassarawa, kuma tana aiki da wata cibiyar karbar magani.

“Wanda ake zargi ta hada kai da wasu miyagu ne domin sace matar, kuma tuni ta amsa laifinsa, mu kuma za mu gurfanar da ita gaban kotu da zarar mun kammala gudanar da bincike.” Inji shi.

Ita ma Paulina ta bayyana ma manema labaru cewa ta aikata laifin, amma tana neman gafara a kan cewa ba za ta sake sikata irin wannan aika aika ba.

A wani labarin kuma, wata mata mai suna Hadiza Bello tare da abokanta guda uku sun gamu da hukuncin daurin shekaru 160 a gidan gyaran halayya biyo bayan kamasu da aka da laifin damfara da kudin bogi, inji rahoton Punch.

Majiyarmu ta ruwaito babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Yola na jahar Adamawa ne ta yanke musu wannan hukunci bayan hukumar yaki da rashawa da makamanta laifuka, ICPC, ta gurfanar dasu a gabanta.

Wata sanarwa daga bakin kaakakin ICPC, Rasheedat Okoduwa ta bayyana cewa Hadiza Bello, Mohammed Daudu, Bello Salisu, Ali Adamu da Hassan Bello sun shirya damfarar wani jami’in kwastam ne, inda zasu bashi naira miliyan 5 na bogi, su kuma su amshi naira miliyan 1 mai kyau.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel