A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa

A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa

Wani mutum da ake zargi da amfani da maganin karin kuzari ya mutu a wani otal da ke Onitsha a jihar Anambra. Kamar yadda rahoton ya bayyana, mutumin ya isa dakin otal din a Onitsha tare da wata budurwa, amma sai budurwar ta fito tana ihun neman taimako.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, SP haruna Mohammed ya ce wajen karfe 12:03 na safiyar 24 ga watan Fabrairun 2020, manajan Plus View otal da ke Onitsha ya kawo koken mutuwar wani a dakin otal dinsu.

Paul Okwudili mai shekaru 40 a duniya na Ogboliolosi da ke babban titin Awka a Onitsha ya kai wata budurwa dakin otal kuma ya mutu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa
A garin neman gira: Matashi ya dirki kwayoyin karin kuzari, ya mutu yana lalata da budurwa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari

Kamar yadda ya ce, manajan ya ce "bayan mintoci da shigarsu tare da budurwar ne ta fito tana ihun neman taimako. Bayan duba shi da muka yi ne muka ga yana numfashi da kyar wanda hakan yasa muka mika shi asibitin St Charles Boromeo da ke Onitsha inda aka tabbatar da mutuwarsa."

Mohammed ya ce jami'an 'yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru sannan sun dau hotunan mamacin.

Kamar yadda ya sanar, babu wani alamun fada a jikin gawar amma an ga wasu magungunan karin kuzari a dakin otal din masu yawa.

An mika gawar mamacin zuwa ma'adanar gawawwaki don duba sanadin mutuwarsa kuma an damke budurwar yayin da ake ci gaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel