Jabun kudi: Kotu ta yanke wa Hadiza Adamu da sauran wasu mutane 3 hukuncin daurin shekara 60

Jabun kudi: Kotu ta yanke wa Hadiza Adamu da sauran wasu mutane 3 hukuncin daurin shekara 60

Wata kotun tarayya da ke zamanta a Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin daurin shekara 60 a gidan yari bayan an gurfanar da su bisa tuhumarsu da mallakar jabun kudi.

Jastis Abdulazeez Anka ne ya yanke wa mutanen hudu, da suka hada da mace guda daya, hukuncin bayan hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rasha wa ta gurfanar da su.

Alkalin ya bayyana cewa zasu shafe shekaru 10 a gidan yari a kan kowanne laifi da suka aikata, kuma kotun ta same su da aikata guda shidda.

A cikin jawabin da kakakin hukumar ICPC, Rasheedat A. Okoduwa, ta fitar, ta bayyana cewa an kama masu laifin da takardun jabun kudi da adadinsu ya kai N5, 504, 000.

"Kamar yadda jami'an ICPC da suka kama masu laifin suka sanar da mu, sun bayyana cewa uku daga cikin masu laifin; Hadiza Adamu Bello, Mohammed Dauda da Bello Salisu, sun bar Kaduna a watan Maris na shekarar 2017 tare da haduwa da cikon mutum na hudu, Ali Adamu, dan jihar Kano tare da dunguma zuwa Wamdeo Uba a jihar Borno domin gana wa da boka, Hassan Bello, wanda zai yi musu kudin jabu na miliyan N5 su kuma su bashi takardun kudi masu kyau na miliyan N1.

"An kama su ne a daidai wurin binciken ababen hawa da ke kan titin Girei zuwa Yola a hanyarsu ta koma wa gida bayan sun dauko kudaden jabu fiye da miliyan N5 da bokan ya yi musu. Jami'an hukumar Kwastam ne suka kama su, suka kuma damka su ga hukumar ICPC," a cewar jawabin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel