Mata 8 da suka taba shugabancin kasa a Afirka

Mata 8 da suka taba shugabancin kasa a Afirka

Mata masu yawa a Afirka sun kasance masu fafutuka da kuma gwawarmaya tamkar maza. Hakan ce kuwa ta sa suke kai wa koluluwar daukaka inda wasu har suka taka matsayin shugabannin kasa dungurungum Ga wasu daga cikin matan da suka samu damar shugabancin kasa baki daya.

Slyvie Kinigi (Mukaddashin shugaban kasar Burundi)

Tayi shugaban kasar Burundi daga ranar 10 ga watan Yuli, 1993 zuwa 7 ga watan Fabrairu 1994. Ita ce mace ta farko da ta fara samun wannan babban matsayin a nahiyar Afirka. A lokacin da ta zama shugaban kasa, ta gyara wasu dokoki tare da tabbatar da wasu sabbi a kan mata,

Ivy Matsepe-Casaburri (Mukaddashin shugaban kasar Afirka ta Kudu)

Gogaggiyar ‘yar siyasar ta kasar Afirka ta kudu ta fara ne a ministan sadarwa. Ta yi mukaddashin shugaban kasa a 2005. Har yanzu kuwa ba a kara yin shugaba kasa mace ba a kasar Afirka ta Kudu tun bayanta. Ta rasu a ranar 6 ga watan Afirilu 2009 lokacin da take da shekaru 71.

Ellen Johnson Sirleaf (Shugabana kasar Liberia)

Mujallar forbes ta sako ta a ta 70 cikin matan duniya masu rinjaye. Ita ce shugabar kasar Liberia ta 24, tayi mulki daga 2006 zuwa 2018. Ta fadi zabe a 1997 inda Charles Taylor yayi nasara.

Rose Francine Rogombé: (Shugaban kasar rikon kwarya ta Gabon)

Tayi mukaddashin shugabar kasar gabon daga watan Yuni na 2009 zuwa watan Oktoba na 2009 bayan mutuwar Shugaban kasa Omar Bongo. Ta kuwa hau wannan matsayin ne bayan da take shugaban majalisar dattijan kasar.

Ta rasu a ranar 10 ga watan Afirilu na 2015 a wani asibiti a Paris inda ta je a duba lafiyarta.

Agnès Monique Ohsan Bellepeau (Mukaddashin shugaban kasar Mauritius)

Sananniyar ‘yar jaridar ta zama mataimakiyar shugaban kasar Mauritius tun 2010. Ta zama mukaddashin shugabar kasar ne a ranar 31 ga watan Maris na 2012 zuwa 21 ga watan Yuli na 2012. Ta sake zama mukaddashin shugaban kasar a ranar 29 ga watan Mayu na 2015 zuwa 5 ga watan Yuni na 2015.

Joyce Hilda Banda (Shugaban kasar Malawi)

Malama ce kuma mai rajin kare hakkin mata. Bayan ta zama ministar harkokin waje daga 2006 zuwa 2009, kuma ta kai matsayin mataimakiyar shugaban kasar Malawi daga watan Mayu na 2009 zuwa Afirilu na 2012.

Ta zama shugaban kasar Malawi bayan mutuwar shugaban kasa Bingu wa Mutahrika. Mujallar forbes ta bayyanata a matsayin mace ta 40 mafi rinjaye a duniya kuma wacce tafi rinjaye a Afirka,

Catherine Samba-Panza ( Mukaddashin shugaban kasar Afirka ta tsakiya)

Samba-Panza ta zama shugaban kasar rikon kwarya ta jamhuriyar Afirka ta tsakiya daga 2014 zuwa 2016. Ita ce mace ta farko a kasar da ta taba hawa wannan babban matsayin kuma ta takwas a Afirka.

Ameenah Firdaus Gurib-Fakim (Shugaban kasar Mauritius)

Ita ce shugaban kasar Mauritius ta shida daga 2015 zuwa 2018. Ita ce mace ta farko da ta zama zababbiyar shugaban kasar Mauritius. Ta fara a matsayin malamar jami’a ne daga nan har ta fada harkar siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel