'Idan dole sai kun yi bara, ba jama'a za ku ke roka ba' - Sarki Sanusi ya bawa almajirai shawara

'Idan dole sai kun yi bara, ba jama'a za ku ke roka ba' - Sarki Sanusi ya bawa almajirai shawara

A ranar Asabar ne mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bawa mabarata da masu neman taimako shawarar cewar su daina rokon jama'a da 'yan uwansu, su mika kokon bararsu ga gwamnati.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Sanusi II ya fadi hakan ne a wurin taron Alarammomi da cibiyar karatun Qur'ani a Najeriya ta shirya mai taken; "tsaftace Almajiranchi domin fuskantar rayuwa ta gaskiya."

Basaraken ya bukaci iyaye su daina tura yaransu makarantun Almajirci, tare da bayyana cewa yara zasu iya koyon karatun Qur'ani a makaruntun unguwanni da garuruwansu.

Sarki Sanusi ya ce idan ya zama dole sai iyaye sun tura yaransu makarantun almajirci, to ya kamata su ke tura su da kayan abinci domin tabbatar da cewa basu zama mabarata ba.

A cewarsa, kuskure ne ga iyaye su tura 'ya'yansu garuruwa da sunan karatu amma ba tare da siya musu komai ba, lamarin da ke saka yaran su koma yin barar abinci da kudi.

'Idan dole sai kun yi bara, ba jama'a za ku ke roka ba' - Sarki Sanusi ya bawa almajirai shawara
Sarki Sanusi II
Asali: UGC

Sarki Sanusi ya janyo ayoyin Qur'ani da zayyana hadisai domin tunatar da masu bara cewa za a tashi mabarata babu nama a fuskarsu ranar tashin kiyama.

DUBA WANNAN: Shagalin bikin Laolu Osinbajo, dan mataimakin shugaban kasa (Hotuna)

Ya kara yin kira ga maza a kan su ji tsoron Allah, su dauki nauyin ciyar da matansu da yara domin kiyaye su daga zama cikin masu bara da neman taimako a wurin jama'a da 'yan uwa.

"Addinin Islama bai yarda da bara ba, idan ma ya zama dole sai mutum ya yi roko, to gwamnati ya kmata ya roka ba jama'ar gari da 'yan uwa ba.

"Ya fi zama alkhairi ga mutum ya je ya saro iatace ya sayar a kan ya yi bara.

"Za a tashi masu roko babu nama a fuskarsu ranar sakamako. Idan ma dole sai mutum ya yi bara, to gwamnati ya kamata ya dosa, domin sune keda alhakin walwalar jama'ar kasa," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel