Ban bada umarnin kama wanda ya siya tsohon layi na ba - Hanan Buhari

Ban bada umarnin kama wanda ya siya tsohon layi na ba - Hanan Buhari

Hanan Buhari, diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta musanta zarginta da ake da cewa ta umarci jami’an tsaron farin kaya na DSS da su damke wani Anthony Okolie a kan amfani da layin wayar da ta taba amfani da shi.

Okolie ya maka hukumar tsaro ta farin kaya a kan take masa hakkinsa da suka yi ta hanyar garkame shi na sama da makwanni 15.

Ya hada da Hanan Buhari tare da MTN a cikin wadanda yake kara tare da bukatar diyyar naira miliyan 500 na take masa hakkinsa da aka yi.

Kamar yadda Okolie ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Asaba, y ace ya siya layin wayar ne a kan naira dubu daya a ranar 8 ga watan Disamba 2018, a kasuwar Ogbeogonogo da ke kan titin Nebu a jihar Delta.

Ban bada umarnin kama wanda ya siya tsohon layina ba - Hanan Buhari
Ban bada umarnin kama wanda ya siya tsohon layina ba - Hanan Buhari
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar nan

Amma kamar yadda rahoton jaridar Premium Times ya bayyana, diyar shugaban kasan ta bayyana cewa, “ana zarginta ne a kan abinda bata san komai a kai ba”.

Kamar yadda lauyanta, M.E Sheriff ya sanar, ta ce: “Ban taba kai korafi gaban hukumar jami’an tsaro ta farin kaya ba ko wata cibiyar tsaro a Najeriya ko wajen kasar nan a kan a kama wani.”

Kamar yadda Hanan ta kara da cewa, “Ba ta da wani matsala idan wani yayi rijista tare da amfani da layin waya da ta taba amfani dashi a shekaru bakwai da suka gabata. Duk da bata ji dadin yadda mutumin ya dinga amfani da layin wayar yana rokon kudi da sunanta ba, bata taba kai wa hukuma kara ba. Bata taba sanin sunan shi Anthony Okolie ba har sai da aka wallafa labarin.”

Nnamdi Dimgba, Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa 3 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel