Za a gabatar da kudurin da za a dinga bawa dalibai aiki da zarar sun kammala bautar kasa

Za a gabatar da kudurin da za a dinga bawa dalibai aiki da zarar sun kammala bautar kasa

- Wani dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Calabar da Odukpani a majalisar tarayya ya mika wata babbar bukata gaban majalisar

- Bukatar ita ce ba duk wanda ya kammala hidimar kasa a Najeriya aikin yi a lokacin da ya kammala

- Hakan zai kawo karshen rashin aikin yi da kuma damfarar ‘yan Najeriya da ake da sunan samar musu da aikin yi

Eta Mbora dan majalisar wakilai ne mai wakiltar mazabar Calabar da Odukpani a majalisar tarayya. Ya mika bukatar a saka dokar ba wa duk wanda ya kammala digiri yayi bautar kasa aiki a kasar nan.

A yayin zantawa da jaridar The Cable a ranar Juma’a, dan majalisar tarayyar ya ce idan aka tabbatar da wannan bukatar za a ba rundunar soji da cibiyoyin da ba na tsaro ba samun ma’aikata a saukake kuma masu karfi a jiki matukar suna da burin karbar aikin bayan kammala hidimar kasarsu ta wajibi.

“Bayan kammala hidimar kasa ta wajibi ta shekara daya, ya kamata a saka wata hanya da cibiyoyi zasu samu masu digirin da ke da bukatar aiki da su. Cibiyoyin zasu iya tantancewa sabbin masu digirin don daukarsu aiki,” ya ce.

KU KARANTA: Babbar magana: Yadda na sha artabu da gawar abokina - Cewar wani mutumi

“Zasu samu aiki suna kammala hidimar kasarsu. Ta wannan hanyar kuma za a iya kawo karshen matsalar rashin aikin yi da kuma damfara da sunan samarwa ‘yan Najeriya aikin yi a kasar nan. Masu bukatar shiga soja ko wasu aiyuka da ba soja ba zasu samu damar yin hakan bayan sun kammala hidimtawa kasa.” Cewar shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel