Kiris ya rage mu gama da Boko Haram da ISWAP: Buratai ya fadawa sojoji

Kiris ya rage mu gama da Boko Haram da ISWAP: Buratai ya fadawa sojoji

Bayan nasarorin da dakarun rundunar sojojin Najeriya suka samu yayin kai farmaki a mabuya da sansanin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP tare da kashe wasu kwamandojin su suka yi, Shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai ya ce nan da kwanaki kadan za a kawo karshen ta'addanci kungiyar Boko Haram.

Bayan hakan, Shugaban sojojin ya kuma taya kwamandojin sansanin sojojin da sauran dakarun sojojin da ke karkashin atisayen Operation Lafiya Dole murna bisa jarumta da suka nuna tare da nasarorin da suka samu a baya bayan nan.

Sakon taya murnar na kunshe ne cikin wasikar taya murna da aka aike wa Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Olusegun Adeniyi da Tukur Buratai da kansa ya saka hannu a kai.

A cikin wasikar, ya yabawa sojojin da kwamandojinsu bisa jarumta da kishin kasa da suka nuna wadda ya yi sanadin halaka shugabanin kungiyar Boko Haram da ISWAP a yankin.

Cikin murna Laftanal Janar Buratai ya ce bai taba murna irin wannan ba a rayurwarsa kuma yana alfahari da sojojin bisa jarumta da kokarin da suka yi wurin kawo karshen ta'addancin Boko Haram da ISWAP.

Kiris ya rage mu gama da Boko Haram da ISWAP: Buratai ya fadawa sojoji
Kiris ya rage mu gama da Boko Haram da ISWAP: Buratai ya fadawa sojoji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar nan

Buratai ya bukaci su cigaba da mamaye yankin tare da gudanar da ayyukansu bisa tsari da doka.

Ya roke su da kada su bawa 'yan ta'addan wata dama ko kadan duk inda suka yi karo da su a yayin da suka gudanar da ayyukansu.

Buratai ya ce wannan jarumtar da suka yi ya karfafa wa 'yan Najeriya gwiwa kuma dama ya san cewa nan da 'yan kwanaki za a kawo karshen 'yan ta'addan na Boko Haram.

Ya tunatar da sojojin cewa, sun taba yi a baya kuma za su iya sake yi ba tare da taimakon wasu sojoji daga kasashen waje ba.

Sanarwar da mukadashin daraktan yada labarai na sojojin, Kanal Sagir Musa ya fitar ta ce Lt Janar Buratai ya tabbatarwa sojojin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai cigaba da basu dukkan goyon bayan da suke bukata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel