Yanzu-yanzu: EFCC ta damke kwamishinan Ganduje

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke kwamishinan Ganduje

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa almundahana, EFCC, ta damke kwamishinan aiyuka na musamman na jihar Kano, Mukhtar Ishaq a kan zarginsa da damfara.

A wata takardar da mai magana da yawun hukumar EFCC din ya fitar a ranar Juma’a, Tony Orilade, ya ce an kama kwamishinan a kan zarginsa da ake da waskar da wasu kudade da aka ware na babban birnin jihar Kano din a yayin da yake shugaban karamar hukumar KMC din.

A wani korafi da aka kai a yayin da yake shugaban karamar hukumar KMC din, an zargesa da waskar da N76,000,000 wanda aka ware don aiyukan ci gaba da tallafawa jama’ar yankin.

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke kwamishinan Ganduje
Yanzu-yanzu: EFCC ta damke kwamishinan Ganduje
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kano: Kotu tayi watsi da bukatar PCACC na dakatar da Sarki Sanusi

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin da yake shugaban karamar hukumar, ya bada umarnin zabtare har N30,000 daga kudin kowacce gunduma ba tare da wani gamsasshen bayani ba.

“Ana zargin kwamishinan da waskar da kadarorin makarantar firamare ta kofar Nasarawa da ke Kano zuwa shaguna, kuma ya siyar da kowanne a naira miliyan goma. Ya kuma waskar da kudaden zuwa amfanin kansa,” EFCC ta ce.

Takardar ta kara da cewa za a gurfanar da Ishaq a gaban kuliya nan ba dadewa in an gama bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel