Gargadi: Yawan shan Paracetamol na iya kashe mutum - Ma'aikaciyar lafiya ta gargadi 'yan Najeriya
- Dr Gbenga Adabusoye babban likita ne a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin wanda yayi karin bayan a kan amfani da magunguna
- Kamar yadda ya sanar akwai bukatar a kiyaye amfani da magunguna ta yadda ya dace don kuwa sukan zama illa babba ga jikin dan Adam matukar aka sha ba yadda ya dace ba
- Ya kara da jan kunnen masu amfani da paracetamol wajen tausasa nama mai tauri ko kuma ganda don gujewa kona kalanzir ko itace
Dr Gbenga Adebusoye babban likita ne a asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin. Ya ja kunne a kan yawan amfani da kwayar paracetamol don yana samar da cutukan hanta da na koda.
Dr Adebusoye ya sanar da hakan ne a tattaunawar da yayi da manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata.
Kamar yadda ya ce, magunguna dai guba ce wadanda ya kamata a dinga amfani da su kadan ba da yawa ba. Suna iya samar da mummunan lahani a jikin dan Adam ko kuma hakan ya zama babbar barazana a rayuwa, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.
Dr Adebusoye ya ce yawan amfani da paracetamol na kawo ciwon hanta kuma yana kashe hanta dukanta matukar ba dashe aka yi ba.
Ya kara da cewa, a daina amfani da paracetamol din wajen yin girki don tausasa abubuwan ci masu tauri domin hakan babban matsala ne ga rayuwa da lafiyar jikin dan Adam.
Ya kara da cewa, akwai kyau a dinga adana magunguna wurare masu matukar sanyi ko madaidaicin sanyi amma babu amfani ajiyesu a waje mai zafi.
KU KARANTA: Tirkashi: Coci taki bari ayi jana'izar wani mutumi akan bai biya kudin taimakon coci na shekara uku ba
Ya ce idan ba a adana magungunan a inda ya dace ba, akwai yuwuwar lalacewarsu wanda kuwa hakan kan zama babban kalubale ga masu shansu.
Hakazalika, akwai yuwuwar lalatattun magungunan su yi aikin da bai da amfani ko kuma wanda zai zama hatsari ga jikin dan Adam.
Dr Adebusoye ya ce ya gano cewa wasu masu siyar da abinci na amfani da paracetamol wajen tausasa nama mai tauri. Ya ce wannan babbar matsala yake zama ga lafiyar jikin dan Adam bayan an ci naman.
Ya shawarci jama’a da su guji amfani da kwayoyi ta yadda bai dace ba don gudun samun matsala babba a bangaren lafiya.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa masu abincin siyarwa a jihar Filato da aka samu zantawa dasu, sun tabbatar da cewa suna amfani da kanwa wajen tausasa ganda ko wake.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng