Tirkashi: Coci taki bari ayi jana'izar wani mutumi akan bai biya kudin taimakon coci na shekara uku ba
- Wata coci a Najeriya ta ki yin bikin birne wani mutum da ya rasu saboda ya dena zuwa cocin na shekaru uku kuma baya bada sadaka
- Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ne ya wallafa yadda aka yi wa mahaifin abokin aikin shi bayan ya rasu
- Cocin sun sanar dasu cewa matukar zasu yi bikin birne shi, toh sai sun biya kudin sadaka na shekaru uku da bai zuba ba
Wata coci a Najeriya ta ki yin bikin birne wani marigayi a cocin saboda ya kai shekaru uku baya zuwa cocin kuma baya bada sadaka na tsawon lokacin da ya dauka baya zuwa bautar.
Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, wani ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita mai suna Kelvin Odanz ne ya wallafa labarin amma bai bayyana kowacce coci bace.
Labarin kuwa ya jawo cece-kuce a kafar daga mutane da dama wadanda suka ce wannan aikin cocin orthodox ne.
Kelvin ya ce mamacin ya kasance mahaifin daya daga cikin abokan aikin shi ne. Ya kara da cewa, cocin ta jaddada cewa sai iyalan mamacin sun biya kudin da bai biya ba na shekaru uku kafin su karbi gawar shi don birne shi.
KU KARANTA: Dr Osei Kwame: Mutumin da ya zama hamshakin miloniya da sana'ar sayar da kaset
Kamar yadda Kelvin ya wallafa: “Mahaifin wani abokin aikina ya mutu amma sai coci suka ce ba zasu jagoranci birne shi ba saboda baya zuwa. Ya kai shekaru uku baya biyan sadakar dole tun bayan da ya dena zuwa.
“Abin ya bani mamaki kuma wannan babban munafinci ne da son kai wanda addinai ke yi kasar nan. Daga karshe dai mun gano cewa duk don kudi ne. Duk tsoron ubangijin da suke ikirari ashe son kansu ya cika musu zuciya.”
Ya kara da cewa, “Idan fasto na bukatar kudi don gina coci ko kuma siyan mota, dukkan ‘yan coci ke hada kudi don daukar nauyin. Amma a lokacin da mutum bashi da lafiya yana gargarar mutuwa, babu cocin da ke tallafawa. Bayan kuma mutum ya mutu sai sun karba daga iyalan shi.”
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng