Abdulhakim Bashir: Matashin da ya kirkiri fasahar da take kama barayi

Abdulhakim Bashir: Matashin da ya kirkiri fasahar da take kama barayi

- Kowanne dan kasuwa na damuwa da yadda kwastomomi ko bata-gari ke satar musu kayayyaki

- Abdulhakim Bashir dan Najeriya ne daga jihar Katsina wanda ya kirkiro wata manhaja da ke tona barawo a shago

- Wannan fasahar ta matashin ta jawo mishi daukaka a duniya inda ya karba lambar yabo a kan wannan kirkirar

Kowanne mai shago na damuwa da yadda kwastomomi ke satar musu kayayyaki don basu iya zama a kowanne kungu na shagon. A shekaru da dama, hakan ya zama babbar matsala ga ‘yan kasuwa amma sai gas hi wani dan Najeriya ya shawo kan matsalar.

Abdulhakim Bashir daga jihar Katsina a Najeriya ya kirkiro Chiniki Guard, wanda ke tona asirin duk wani abin zargi ko na sata zuwa wata manhaja a wayar tafi da gidanka.

Abdulhakim Bashir: Matashin da ya kirkiri fasahar da take kama barayi
Abdulhakim Bashir: Matashin da ya kirkiri fasahar da take kama barayi
Asali: Facebook

A 2019, Abdulhakim Bashir ya yi nasarar lashe gasar AI Startup inda ya karba lambar yabo bayan ya bayyana fasahar shi a GITEX 2019 wanda ake yi duk shekara a Dubai.

Ya bayyana a wanda ya lashe gasar AI a cikin mutane 157 daga kasashe 73 na duniya.

KU KARANTA: Allah Sarki: Gobarar gas ya kashe Amarya kwanaki 27 kacal da bikinta

Abdulhakim Bashir mutum ne mai hazaka da aka bayyana a zangon First Class Material, wanda ke nuna aiyukan ban mamaki da hazaka da ‘yan Najeriya ke yi a gida da wajen kasar nan.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito, Bashir ya ce ya samu kwarin guiwar samar da abinda zai hana satar ne tun bayan da ya fara kerar Chiniki, wata hanyar kasuwanci ne a yanar gizo.

Daga nan ne ya gano cewa babbar matsalar masu siyar da kayayyaki ba a yanar gizo take ba, tana wajen tafiyar da kasuwancin ne da kuma satar da ake musu. Ya kirkiro da manhajar ne don taimakawa ‘yan kasuwa.

Tun da wannan manhajar ta bayyana, ta shawo kan matsaloli manya kuma ta sa ya kara suna a duniya baki daya.

Hakazalika, Bashir ya dau ‘yan Najeriya aiki daga Arewa masu yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel