Allah Sarki: Gobarar gas ya kashe Amarya kwanaki 27 kacal da bikinta

Allah Sarki: Gobarar gas ya kashe Amarya kwanaki 27 kacal da bikinta

- Bayan kwanaki 27 da auren Sa’adatu Muhammad Babangida da angonta Najib Ahmed ne mummunan lamarin ya faru da amarya

- Sa’adatu tayi korafin ciwon hakori ne wanda yasa ta tafi madafi neman magani amma sai salatinta da salallaminta ango Najib ya ji

- Bayan kwanakin da ta shafe a asibiti sakamakon konewar da tayi daga fashewar tukunyar gas, ta ce ga garinku a wata ranar Litinin

A ranar 12 ga watan Janairu na 2020 ne, wanda yayi dai-dai da kwanaki 27 da auren Sa’adatu Muhammad Babangida da angonta Najib Ahmed, mummunan lamarin ya faru. Wajen karfe 10:30 na dare ne Sa’adatu ke korafin ciwon hakori wanda hakan yasa ta je madafi neman mafita. Bayan wani lokaci ne ango Najib ya ji fashewar wani abu wanda ya girgiza dukkan gidan.

“Na fara jin Sa’adatu na cewa Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Daga nan na zargi cewa wani mummunan lamari ya faru da matata.” In ji Najib.

Allah Sarki: Gobarar gas ya kashe Amarya kwanaki 27 kacal da bikinta
Allah Sarki: Gobarar gas ya kashe Amarya kwanaki 27 kacal da bikinta
Asali: Facebook

Ya sameta cikin madafin da rabin jikinta a kone. A take aka gaggauta kaita asibitin koyarwa na Jos da fatan samun lafiyarta. A ranar 3 ga watan Fabrairu kuwa ta ce ga garinku sakamakon munanan raunikan da ta samu daga kunar gas din.

Mahaifiyarta mai suna Hadiza Muhammad Babangida ta sakanknace cewa diyarta za ta warke don ganin yadda ta ke samun sauki, kamar yadda jaridar Gistmania ta wallafa.

KU KARANTA: Bidiyo: Daliban Sakandare sun yiwa Malamin su dukan tsiya a jihar Katsina

“Karshen ganin da nayi wa Sa’adatu shine ranar Asabar, 1 ga watan Fabrairu lokacin da naje ziyartarta. Tana murmushi ni kuwa ina kara mata karfin guiwar cewa za ta warke. Nayi mata addu’o’i kafin daga baya in tafi gida don shaidawa ‘yan uwa cewa tana samun sauki,” Mahaifiyarta ta ce.

Bayan kwanaki biyu ne da kaimata ziyara aka kirata a waya tare da sanar mata cewa diyarta ta rasu.

Sa’adatu ta rasu tana da shekaru 30 a duniya. Ta kammala karatun digirinta na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma tana cikin ma’aikatan N-Power.

Mahaifiyarta ta shaida cewa Sa’adatu na matukar kyautata mata tare da tallafar danginta da albashinta da take samu.

Angon Sa’adatu ya shaida kyawawan halayen matar shi domin kuwa ya ce ko bayan da aka kaita asibitin, ta nuna farin cikinta ta yadda wannan hatsarin bai ritsa da shi ba.

“A cikin shekara daya da haduwarmu, mun fada son juna sosai ta yadda muka yi aure amma ashe ba zamu zauna tare har abada ba.” Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel