Matar da ta zama mataimakiyar shugaban makarantar sakandare daga aikin shara da goge-goge

Matar da ta zama mataimakiyar shugaban makarantar sakandare daga aikin shara da goge-goge

- Pam Talbert, mataimakiyar shugaban makarantar sakandare na Istrouma Middle, ta burge mutane da dama yadda ta tashi daga mai shara zuwa wannan matsayi da take da shi a yanzu

- Talbert mai yara guda uku, tana da matsala a fannin fahimtar karatu, amma 'ya'yanta suka shawarce ta akan ta dage ta koma makaranta

- Yanzu haka malamar ta kammala digiri na farko dana biyu a jami'ar Southern University

Wata mata daga kasar Amurka ta zama abar kwatance wajen jajircewa, bayan ta kai wani babban matsayi a wajen aikinta.

Pam Talbert wacce tayi aiki a makarantar a matsayin mai shara da goge-goge ta kai matsayin mataimakiyar shugaban makarantar a yanzu.

A rahoton WBRZ, matar na da matsalar fahimta a fannin karatu, amma hakan bai hana ta cimma burinta ba.

Matar da ta zama mataimakiyar shugaban makarantar sakandare daga aikin shara da goge-goge
Matar da ta zama mataimakiyar shugaban makarantar sakandare daga aikin shara da goge-goge
Asali: Facebook

Ga mutumin da bai iya karatu da rubutu ba, ya kai wannan matsayi ba karamin abin mamaki bane.

"Abubuwan mamaki na faruwa a duniya, kuma kuna kallon shi, ni misali ce ta mu'ujiza. Ban iya karatu da rubutu ba a da," ta ce.

KU KARANTA: 'Yar shekara 7 ta tara naira miliyan daya da rabi tana biyawa abokanan ta talakawa kudin abinci a makaranta

Pam ta bayyana cewa 'ya'yanta guda uku sune suka taimaka mata wajen cikar wannan buri nata.

Matar tana karatu tare da 'ya'yanta idan sun dawo daga makaranta, har ta samu ta fara tsintar wasu abubuwa daga cikin abinda ake koya musu.

Lokaci da dama idan sun dawo daga makaranta suna koyawa mahaifiyar ta su karatu.

A hankali a hankali ta samu ta fara tsintar wasu abubuwa har ta kai matsayin da ta kammala karatun digiri na farko dana biyu a Southern University.

"Ba abu bane mai sauki a gareni, amma na jajirce saboda na san cewa wannan abu ne mai muhimmanci a wajena," cewar Pam.

Wani abin burgewa kuma shine, yanzu haka Pam da danta sun koma jami'a domin karantar digirin digirgir a Southern University.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel