Yan bindiga sun bude ma Yansanda wuta a shingen binciken ababen hawa

Yan bindiga sun bude ma Yansanda wuta a shingen binciken ababen hawa

Akalla jami’an Yansanda guda biyu ne suka rasa rayuwarsu bayan wani mummunan hari da wasu gungun miyagun yan bindiga suka kaddamar a wani shingen binciken ababen hawa dake karamar hukumar Irele ta jahar Ondo.

Jaridar TheCable ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ondo, Femi Joseph ya bayyana an kashe Yansandan ne a kan titin Ajagba a ranar Litinin, 17 ga watan Feburairun shekarar 2020.

KU KARANTA: Hukuncin kisa: Maryam Sanda ta kalubalanci hukuncin a kotun daukaka kara

Femi ya ce tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka kai wannan hari, sa’annan ya kara da cewa akwai wani jami’in dansanda daya da ya samu rauni a sanadiyyar harin, kuma yana samun kulawa a asibiti.

“Mun yi asarar jami’anmu guda biyu a ranar Litinin, amma bamu san ko su wanene suka kai harin ba, bamu sani ba ko yan fashi ne, ko yan bindiga ne ko kuma yan baranda ne kawai, har sai mun kamasu ne zasu tabbatar mana ko su wanene.” Inji shi.

A wani labarin kuma al’ummar garin Uratta na karamar hukumar Owerri ta Arewa na jahar Imo sun rushe gidaje guda uku mallakin wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, Okechukwu Uche biyo bayan mutuwar matar babban basaraken garin, Uwargida Ugoeze Comfort Okoro.

A yanzu haka Uche yana gidan yari na jahar Imo, amma jama’an garin sun tabbatar da cewa shi ne ya shirya yadda aka yi garkuwa da matar Sarkinsu, ma shekaru 76 a rayuwa, wanda daga bisani aka kasheta bayan an biya kudin fansa.

Wannan ne ya harzuka jama’an suka fuskanci gidajen Uche a fusace har sai da suka sauke dukkaninsu guda uku daga sama har kasa.

Ita ma rundunar Yansanda reshen jahar Imo ta bayyana Uche a matsayin wanda ya shirya kisan matar, amma sun musanta hannu cikin rusa gidajensa, kamar yadda kaakakinta, Orlando Ikeokwu ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel