Najeriya kasa ce mara alkibla - Sanatan PDP

Najeriya kasa ce mara alkibla - Sanatan PDP

Mathew Urhoghide, sanatan Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar PDP daga jihar Edo, ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da alkibla idan aka zo fannin tsari. Urhoghide ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin bada gudumawa a kan wata tattunawa da Stella Oduah, sanata mai wakiltar jihar Anambra ta Arewa ta mika gaban majalisar.

Oduah ta bayyana bukatar kirkirar kasafin kasar nan mai tsarin hangen nesa. A yayin jawabin sanatan daga jihar Edo, ya ce Najeriya ba ta bada fifiko a wajen kasafin kudi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

“Idan ka duba asarar da ke kunshe a cikin kasafin kudinmu na kowacce shekara za ka gane cewa tabbas babu alkibla. Idan aka hada jimillar kudin, za ka yi tunanin ba a san abinda za a yi da kudin bane bayan ga abubuwa da yawa da ke bukatar a dubasu,” ya ce.

Najeriya kasa ce mara alkibla - Sanatan PDP
Najeriya kasa ce mara alkibla - Sanatan PDP
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare

“Domin tabbatar da cewa Najeriya ba ta da alkibla idan aka zo tsari, ko bangaren kiwon lafiya da ake bukatar a ba fifikon kashi 15 ba a dubawa. Tun zuwa na majalisar dattijai a 2015, ban taba ganin an yi hakan ba. Ba sai kasa na da tarin tattalin arziki ba ake tsarin ci gaba, kana yin komai ne daidai da yadda kake da shi.” In ji shi.

“Muna ta zancen wuta a kasar nan, babu wanda zai ce yana samun wuta yadda ya kamata.” Ya kara da cewa.

A yayin jagorantar tattaunawar, Oduah ta ce a shekaru 20 da suka gabata, kasar nan na shirya tsare-tsaren da basu aiki kwata-kwata.

“A bayyane yake cewa tsare-tsaren sun kasa kai Najeriya inda take bukata na zama daya daga cikin manyan kasashe 20 na duniya masu tarin tattalin arziki a duniya,” cewar Oduah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel