Amurka ta sahale wa sojojinta Musulmai barin gemu, saka hijabi da yin rawani

Amurka ta sahale wa sojojinta Musulmai barin gemu, saka hijabi da yin rawani

Rundunar sojojin sama ta kasar Amurka ta bawa dakarunta Musulmi izinin tara gemu da saka hijabi yayin da suke cikin kakinsu na sojoji.

A cewar sabon bayanin da rundunr ta fitar, ta bawa dakarunta mabiya addinin Sikh damar yin rawani, kamar yadda kafar yada labarai ta CNN ta rawaito.

A sabuwar dokar sabon tsarin saka kaya a rundunar sojin, mabiya addinin Sikh da Musulmai zasu iya neman 'yancinsu na addini domin yin rawani, barin gemu da amfani da hijabi kuma za a amince da bukatarsu matukar shigarsu bata nuna cewa akwai zazzafar akidar addini ba.

Zai dauki rundunar sojin kwana 30 kafin ta amince da bukatar soja na neman amfani da rawani, hijab ko barin gemu yayin aiki a cikin kasar Amura. Zai dauki kwana 60 idan a wajen kasar Amurka ne.

A baya a kan dauki lokaci mai tsawo kafin rundunar soji ta amince da bukatar mabiya addinin Sikh da Musulunci na yin shiga da ke nuna addininsu.

Sabuwar dokar da aka kirkira ta kayyade adadin mafi yawan kwanakin da bukatar dakarun soji Musulmai da Sikh za ta yi, sabanin yadda ake daukan lokaci mai tsawo kafin amince wa da bukatar a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel