'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga - zanga a kan ritayar dole ga sojoji

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga - zanga a kan ritayar dole ga sojoji

A ranar Alhamis ne 'yan sanda a kasar Sudan suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga - zangar neman a mayar da sojojin da aka yi wa ritayar dole bakin aikinsu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya sanar.

An sallami sojojin daga bakin aiki ne bayan sun nuna goyon bayansu ga juyin - juya hali da aka yi a kasar.

"Daruruwan matasa ne suka gudanar da zanga - zanga a daura da fadar shugaban kasa. Matasan na dauke da rubutaccen sakon nuna rashin amincewa da korar sojojin daga bakin aiki," a cewar wakilin AFP.

Masu zanga - zangar sun rufe hanya tare da kona taya a kan kwalta kafin daga bisani jami'an 'yan sanda su yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su.

A farkon makon nan ne rundunar sojojin kasar Sudan ta fitar da jerin wasu manyan sojoji da ke rike da mukamai daban - daban tare da bayyana cewa ta yi musu ritayar dole.

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga - zanga a kan ritayar dole ga sojoji
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga - zanga a kan ritayar dole ga sojoji
Asali: Twitter

Kakakin rundunar sojin kasar, Amer Muhammad Al-Hassan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Sudan (SUNA) cewa rundunar sojin ta fitar da sunayen sojojin ne kamar yadda ta saba a kowanne farkon shekara.

DUBA WANNAN: Abinda ya hana mu bude wa mayakan Boko Haram wuta yayin harin Garkinda - NAF

Sai dai, masu rajin kare hakkin bil adama sun fara gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da korar sojojin, musamman laftanal Mohammad al-Sadiq, da suka goyi bayan juyin juya halin da aka fara a watan Disamba na shekarar 2018.

Kungiyar kwararrun kasar Sudan, wadanda suka shurya zanga-zangar hambarar da tsohon shugaba Bashir, sune suka shirya zanga-zangar ta ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel