Gwamnatin Jigawa ta karbi bashin $37m daga bankin cigaban musulunci IDB

Gwamnatin Jigawa ta karbi bashin $37m daga bankin cigaban musulunci IDB

Gwamnatin jihar Jigawa ta karbi bashin $37m daga bankin cigaban Musulunci IDB domin gudanar da ayyukan raya karkara a jihar.

Gwamnan jihar, Muhammadu Badaru Abubakar, ya sanar da haka ne ranar Laraba a wajen kaddamar da faruwar aikin a maaikatar noma da raya karkara wato JARDA, a birnin Dutse.

Yace manufar karbar bashin itace karfafa abubuwan da jihar ta cimma akan noma da samar da aiki a watanni hudu da suka gabata.

Badaru yace aikin zai samarwa matasa kimanin miliyan biyu aiyuka a Jihar.

Gwamnatin Jigawa ta karbi bashin $37m daga bankin cigaban musulunci IDB
Gwamnatin Jigawa ta karbi bashin $37m daga bankin cigaban musulunci IDB
Asali: Depositphotos

KU KARANTA Harin Chibok: Soja ya rasa kafarsa, an nemi biyu an rasa

Gwamnan yayi bayanin cewa aikin ya kunshi bangarori daban-daban wanda suka hada da samar da ruwa ga gonaki, , kasuwanci da taimako daga kananan bankuna.

”Aikin zai taimaka akan bangarori da dama na inganta noma, kamar samar ma shuka ruwa, kiwon kifi, bunkasa filaye, gina hanyoyi, gina kasuwanni da fayyace hanyoyin wucewan dabbobi” gwamnan ya bayyana.

Badaru yace gwamnatin jihar zata taimakawa kananan manoma da yan kasuwa bashi daga bankuna .

Ya bada tabbacin cewa wadanda zasu amfana da wannan zasu biya saboda kashi 75% zuwa 80% da suka amfana a baya sun biya.

Mai wakiltar bankin cigaban muslunci, Mayo Miyary ya tabbatar da taimako da hadin kan gwamnati akan noma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel