Rikicin ma’aurata: Lebura ya kashe matarsa da mugun duka a jahar Legas

Rikicin ma’aurata: Lebura ya kashe matarsa da mugun duka a jahar Legas

Rundunar Yansandan Najeriya, reshen jahar Legas ta kama wani mutumi mai sana’ar Leburanci, John Onyeama dan shekara 50 a rayuwa a kan zarginsa da kashe matarsa Esther ta hanyar lakada mata dan banzan duka.

Sai dai Daily Trust ta ruwaito John mai sana’ar Leburanci ya dage kai da fata cewa lallai fa matarsa ta mutu ne a sakamakon bugawar zuciya, ba kamar yadda Yansanda suke zarginsa da lakada mata dan banzan duka wanda ya yi sanadiyyar ajalinta ba.

KU KARANTA: Yansanda sun ki karbar cin hancin N700,000 daga hannun barayin shanu a Sakkwato

Amma Yansanda sun ce binciken likitoci a asibiti ya nuna cewa Esther, wanda ita ce mai makarantar Brillianta Kids Nursery and Primary Schools, ta mutu ne a sanadiyyar raunuka da ta samu daga mugun duka da ta sha a wajen mijinta.

Ko da yake shi ma John ya bayyana cikin jawabin daya katabta cewa: “Mun dade muna samun matsala a tsakaninmu, har ma ta kwashe kayanta daga gidana kawai don bani da kudi, sai ta koma gidan wani Fasto tana zama, ina zargin ma suna kwanciya da junansu.

“Kafin faruwar lamarin nan, wata rana a cakin watan Janairu na dawo gida kwatsam sai na tarar matata bata nan, sai yaranmu kawai na tarar a gidan, kwana na uku ina nemanta, sai a rana na hudu ne na gano ta koma gidan wani Fasto, da na je gidan sai na tarar da ita da daurin kirji, shi kuma Faston da gajeren wando.

“Amma da na yi kokarin mata magana, sai Faston ya lakada min dan banzan duka, ya koreni daga gidansa. Duk kokarin da na yi don ganin ta koma gidana ya ci tura, sai a ranar 16 ga watan Janairu na sameta a makarantarta.

“Na yi kokarin yi mata magana, amma bata saurareni ba, daga nan muka fara cacar baki har na tafi, wannan shi ne gani na karshe da na mata, bayan kwanaki 3 na samu labarin wai matata tana asibiti, zuwana asibitin keda wuya na tarar ta mutu.” Inji shi.

Sai dai Yansanda sun bayyana cewa John na zargin Esther da neman maza da kuma hana shi daman kwanciya da ita, don haka suka ce zasu gurfanar da shi gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel