Babu saura ciwon zuciya: An gano maganin ciwon 'soyayya

Babu saura ciwon zuciya: An gano maganin ciwon 'soyayya

Dakta Alain Brunet, wani mai bincike, ya bayyana cewar ya gano wata hanya da wadanda suka rabu da masoyi ko masoyiya zasu manta tare da shafe tunanin masoyin kuma ba tare da wata wahala ba.

A cewar Dakta Brunet, ya shafe a kalla shekaru goma sha biyar yana nazari a kan mawuyacin halin kunci da damuwa da ke biyo bayan rabu wa da masoyi ko masoyiya.

Dakta Brunet ya ce hanyar da ya gano ita ce hanyar lallami da bayar da shawara, hanyar da ya ce ya gano ta ne sakamakon aikin da ya yi tare da kwararru a kan soyayya da kuma mu'amala da wadanda suka taba tsintar kansu a cikin irin matsalar ciwon 'soyayya'.

Ba iya shawara da lallami ne kadai maganin ciwon 'soyayya' ba, Dakta Brunet ya ce kwayar maganin bature mai suna 'propanalol' ta na taimaka wa wajen maganin ciwon zuciya da hawan jini.

Babu saura ciwon zuciya: An gano maganin ciwon 'soyayya
Babu saura ciwon zuciya: An gano maganin ciwon 'soyayya
Asali: UGC

A bisa tsari, idan mutum ya kamu da ciwon so, za a fara bashi kwayar 'Propanalol ya fara sha sannan bayan sa'a guda sai a fara bashi shawarwari.

A wurin bayar da shawarar, za a bukaci wanda ke fama da ciwon so ya rubuta irin abinda ke damunsa sannan ya karanta da karfi a bayyane.

DUBA WANNAN: An bayyana abinda cire su Buratai zai haifar a Najeriya

Kwayar Proparanolol ta na taimaka wa wajen rage radadi da zugi irin na soyayya da kuma tunanin abubuwan da suka faru yayin soyayyar.

Ya zuwa wannan lokaci, an yi wa kimanin mutaner 400 maganin 'ciwon so' ta hanyar amfani da dabarar Dakta Brunet.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng