Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara

Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta bankado wasu wurare biyu da ke Kaura-Namoda da Sakajiki inda ake zargin wajen boye shanun sata ne a jihar.

Kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida, Abubakar Dauran, ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan duba gine-ginen a ranar Laraba.

"A yau mun zo Kaura Namoda ne da Sakajiki don ganin inda ake boye shanun sata. Wajen na Kaura Namoda mallakin wani Abdurrahman Isah ne yayin da na Sakajiki yake mallaki Abdurrahman Loko," in ji shi.

Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara
Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Matawalle ya dauki mataki kan hukuncin kisa da Saudiyya ta yanke wa Malamin Najeriya

Dauran ya ce an kama wasu shanun satan daga karamar hukumar Zurmi a wajen.

Kwamishinan ya sanar da cewa duk da kokarin gwamnatin wajen shawo kan matsalar tsaro a jihar, wasu miyagu na ci gaba da shiga mugun aikin da kansu.

"Zamu nemi alfarma daga gwamnatin jihar nan don mu rushe gine-ginen. Mun kama mai gidan na Kaura Namoda amma na Sakajiki bai riga ya shiga hannu ba. Zamu tabbatar da cewa mun damko shi kuma anyi bincike mai kyau tare da gurfanar da su," ya ce.

Daga bisani ya ja kunnen masu kaiwa 'yan ta'addan bayanan sirri da su gujewa hakan don matukar aka kamasu, zasu fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel