Babbar magana: Maza ne suka kirkiro addini kawai dan su dinga zalintar mata - Efia Odo

Babbar magana: Maza ne suka kirkiro addini kawai dan su dinga zalintar mata - Efia Odo

- Bayan rubutun da ta wallafa a makon da ya gabata na cewa bata yadda da cewa akwai wuta da aljannah ba

- Fitacciyar jarumar 'yar kasar Ghana a wannan karon ta fito da wani sabon salon labari kuma

- Jarumar ta ce maza ne kawai da son zuciyar su suka kirkiri addini domin su dinga juya mata, amma wanda ya halicci duniya bai ce ayi wani addini ba

Fitacciyar jarumar nan ‘yar kasar Ghana, Efia Odo ta bayyanawa wata magana a shafinta na Instagram akan addini.

Jarumar a cikin rubutun da ta wallafa cewa: “Wanda ya hallici duniya bashi da wani addini.” Sannan ta kara da cewa maza ne suka halicci addini domin su dinga juya mata yadda suke so.

Jarumar ta kawo hujja akan wannan magana da tayi, inda ta ce: “Babu mala’ika ta mace duk maza ne,” ta ce addini ya bawa bangare daya karfi.

Ga dai abinda jarumar ta rubuta a kasa:

Babbar magana: Maza ne suka kirkiro addini kawai dan su dinga zalintar mata - Efia Odo
Babbar magana: Maza ne suka kirkiro addini kawai dan su dinga zalintar mata - Efia Odo
Asali: Facebook

Fitacciyar jarumar 'yar asalin kasar Ghana tayi kaurin suna wajen jawo kace nace a shafukan sada zumunta.

Jarumar ta kan fito shafukan sadarwa ta kwaba maganar ta yanda take so, sai dai amma tafi yawan yin magana akan abubuwan da ya shafi addini.

Idan ba a manta ba a makon daya gabata mun kawo muku wani labari na yadda jarumar ta fito ta bayyana cewa ta yadda akwai Allah, amma kuma zancen cewa akwai wuta da Aljannah, duk labarin kanzon kurege ne a wajenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel