Za’a shiga wahalar mai a Kano, Katsina da Jigawa dalilin yajin aikin direbobin tanka

Za’a shiga wahalar mai a Kano, Katsina da Jigawa dalilin yajin aikin direbobin tanka

Kungiyar direbobin tankar mai, PTD da kungiyar direbobin motocin haya, NARTO sun fara yajin aikin sai baba ta ji a ranar Talata, 18 ga watan Feburairu sakamakon cin zarafi da suka ce jami’an hukumar kwastam suna yi ma mambobinsu.

Daily Nigerian ta ruwaito kememe direbobin sun ki daukan mai daga depot din Kano, wanda yake shayar da jahohin Katsina, Kano da Jigawa man fetir, haka nan sun yi watsi da tashar mai ta Gusau, dake baiwa Zamfara, Sakkwato da Kebbi mai.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Monguno ya zargi Abba Kyari da kawo cikas ga kwangilar sayen makamai

Shugaban NARTO, Yusuf Othman ya bayyana cewa sun fara yajin aikin ne saboda cin mutuncin direbobinsu da jami’an hukumar kwastam suke musu, tare da kama musu motoci dauke da kaya a Kano, Kebbi, Katsina da sauran jahohin Najeriya.

A cewar Othman, kwastam suna fakewa ne da dokar hana shigar da man fetir zuwa kilomita 20 daga iyakokin Najeriya. “Amma kwararan hujjoji sun tabbatar da dukkanin kamen da kwastam suke ma direbobinmu a cikin gari ne. Musamman ma motocinmu 5 da aka kama a Kano, wanda nisansu daga kowanne iyakar Najeriya ya haura akalla kilomita 200.” Inji Othman.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban PTD, Sa’idu Al’amura ya bayyana cewa kungiyarsu ta ga dacewar shiga yajin aiki domin nuna damuwarta game da cin zarafin mambobinta da ake yi yayin da suke kan hanyarsu ta kai mai gidajen mai a Kano.

Don haka yace sun umarci dukkanin mambobinsu dake jahohin Jigawa, Katsina, Sakkwato, Kebbi da Zamfara da su fara yajin aikin dindindin har sai an warware matsalar dake tsakaninsu da kwastam.

Ya kara da cewa yayin da suke yajin aikin, babu wata motar dakon mai da zata yi lodi zuwa wani gidan mai a duk fadin jahohin 6, har sai hukumar kwastam ta sakar musu motocinsu da jami’anta suka kama.

Shi kuwa, mai magana da yawun hukumar kwastam reshen jahohin Kano/Jigawa, Danbaba Isah ya tabbatar da kama motocin 5, kuma yace sun kamasu ne da laifin karkatar da mai daga Kano zuwa Fago a karamar hukumar Sandamu na jahar Katsina.

Sai dai yace bayan gudanar da bincike sun saki mota daya sakamakon sun gane cewa yana kai ma wani dan kwangila mai ne dake aikin titi a Jigawa, amma yace sauran direbobin hudu suna hannu, kuma zasu gurfanar dasu gaban kotu da zarar sun kammala bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel