Duniya makwanta rikici: An kama budurwa da auren Mazaje 2 a jahar Ebonyi

Duniya makwanta rikici: An kama budurwa da auren Mazaje 2 a jahar Ebonyi

Duniya makwanta rikici in ji masu iya magana, an gurfanar da wata budurwa yar shekara 22, Nkeiruka Winifred tare da wasu maza biyu Chijoke Obasi dan shekara 47 da Stanley Mbam dan shekara 30 gaban wata kotun majistri dake Abakaliki, jahar Ebonyi.

Punch ta ruwaito rundunar Yansandan jahar Ebonyi na tuhumar mutanen uku ne da kulla haramtaccen alakar aure a tsakaninsu, wanda hakan ya saba ma kundin dokokin zamantakewa na jahar Ebonyi.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Monguno ya zargi Abba Kyari da kawo cikas ga kwangilar sayen makamai

An zargi budurwa Winifred da laifin kulla aure tsakaninta da Stanley Mbam, duk kuwa da cewa akwai igiyar aure tsakaninta da Dakta Solomon Nwankwo. Mutanen uku sun aikata laifin ne a unguwar Hausa Quarters da titin Mbam, cikin karamar hukumar Abakaliki a ranar 26 ga watan Oktoban 2019.

Hakan ta sa rundunar Yansandan jahar Ebonyi ta tasa keyarsu duka gaban kuliya manta sabo a ranar Litinin, 18 ga watan Feburairu, inda take tuhumarsu da aikata laifuka guda uku da suka danganci hadin baki, aure biyu a tare da kuma zamba cikin aminci.

Dansanda mai shigar da kara, ASP Mathias Eze ya shaida ma kotu cewa doka ta tanadi hukunci ga laifin da mutanen uku suka tafka a sashi na 516A (a), 370 da 419 (A) na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Ebonyin Najeriya na shekarar 2009.

A wani labarin kuma, kungiyar direbobin tankar mai, PTD da kungiyar direbobin motocin haya, NARTO sun fara yajin aikin sai baba ta ji a ranar Talata, 18 ga watan Feburairu sakamakon cin zarafi da suka ce jami’an hukumar kwastam suna yi ma mambobinsu.

Kememe direbobin sun ki daukan mai daga depot din Kano, wanda yake shayar da jahohin Katsina, Kano da Jigawa man fetir, haka nan sun yi watsi da tashar mai ta Gusau, dake baiwa Zamfara, Sakkwato da Kebbi mai.

Shugaban NARTO, Yusuf Othman ya bayyana cewa sun fara yajin aikin ne saboda cin mutuncin direbobinsu da jami’an hukumar kwastam suke musu, tare da kama musu motoci dauke da kaya a Kano, Kebbi, Katsina da sauran jahohin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel