Cin amana: Budurwa ta sayar da motar da saurayinta ya bata kyauta ta yi shirin auren wani da kudin

Cin amana: Budurwa ta sayar da motar da saurayinta ya bata kyauta ta yi shirin auren wani da kudin

- Wani mutum mai suna Dr. Max ya bayyana irin cin amanar da wata budurwa tayi wa abokin shi

- Bayan daukar dawainiyar karatunta, ciyarwa, kudin haya da komai,sai ya siya mata motar hawa

- Bayan kammala karatu ne ta je gida inda aka sa mata rana da wani tare da siyar da motar don daukar dawainiyar bikin

Wani mutum dan Najeriya mai suna Dr. Max Vayshia ya je shafin shi na tuwita inda ya wallafa halin cin amanar da budurwa ta gwada wa abokin shi.

Kamar yadda Max ya sanar, abokin shi ya fara soyayya da budurwar ne tun a watan Janairu na 2017. Shi ya dau nauyin budurwar na makaranta sannan daga bisani ya siya mata mota kirar Toyota Corolla. Ya kara da kama mata haya tare da zuba mata kayayyakin da take bukata, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.

A haka dai ta dinga cewa ba zasu kwanta ba har sai sun yi aure kuma ya kiyaye sharadinta.

A wani lokaci kankani sai ta ce za ta je gida ganin iyayenta amma daga nan sai ya dena jin wayarta. Duk iya kokarin shi amma shiru.

KU KARANTA: Allah mai iko akuya ta haifi dodo bayan an yi mata tiyata

Bayan wani lokaci, sai ya samu labarin an sa ranar aurenta ne kuma ta siyar da motar da ya siya mata ne don daukar nauyin bikinta da masoyinta. Ta kara da ba da hayar gidan da take ciki.

Kamar yadda Max ya wallafa: "Abokina ya fara son wata farar yarinya a watan Janairu na 2017 kuma tun daga nan soyayya ke yin karfi. Ya samar mata gurbin karatu a babbar makaranta kuma yana biya mata kudin makaranta. Shi ke ciyar da ita kuma gidan da take shi ya kama tare da zuba mata kayan bukatunta. Bayan kammala karatunta ne ya siya mata mota kirar Toyota Corolla. Budurwa ta ce za ta je gida amma tun bayan tafiyarta sai ya ji shiru. Daga baya ne ya gano aure za ta yi kuma ta siyar da motarta don daukar dawainiyar bikin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng