Masoyan Trump sun zazzagi 'yarshi da ta sanya Hijabi lokacin da ta kai ziyara Masallaci

Masoyan Trump sun zazzagi 'yarshi da ta sanya Hijabi lokacin da ta kai ziyara Masallaci

- Magoya bayan Shugaban kasar Amurka, Donald Trump sun juyawa Ivanka Trump baya ganinta sanye da hijab da suka yi

- Ivanka Trump diya ce kuma mai bada shawara ta musamman ga Shugaban kasar Amurka, Donald Trump

- Ta je daular larabawa ne don halartar wani taro inda daga baya yariman kasar mai jiran gado ya zagaya da ita babban masallacin kasar

Masoyan shugaban kasar Amurka, Donald Trump sun caccaki 'yar shi Ivanka Trump, bayan ta sanya Hijabi a lokacin da ta kai ziyara Dubai.

An ga hotunan Ivanka dai suna ta yawo a shafukan sada zumunta sanye da Hijabi, a lokacin da ta kai ziyara hadaddiyar daular Larabawa, hakan ya sanya magoya bayan mahaifinta cikin mamaki da rudu.

Diya a wajen shugaban kasar Amurka din, sannan kuma mai bayar da shawara a gareshi ta musamman, ta kai ziyara hadaddiyar daular Larabawan a ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Ta halarci wani taron tattaunawa na manyan matan duniya da aka gabatar a kasar. Daga wajen taron kuma ta gana da Yariman kasar mai jiran gado, Sheikh Mohammed bin Zayed Al-Nahyan.

Masoyan Trump sun zazzagi 'yarshi da ta sanya Hijabi lokacin da ta kai ziyara Masallaci
Masoyan Trump sun zazzagi 'yarshi da ta sanya Hijabi lokacin da ta kai ziyara Masallaci
Asali: Facebook

Kowa dai ya san cewa Ivanka Trump ba bakuwa bace a kasar ta Dubai, to amma an ga hotunanta tana yawo sanye da Hijabi, lokacin da Yariman kasar yake zagayawa da ita a cikin babban Masallacin kasar.

Wannan lamari ya kawo zage-zage da maganganu na rashin kirki ga 'yar gidan shugaban kasar ta Amurka, inda suke cewa tana goyon bayan Musulmai ne na bogi

Da yawa daga cikin magoya bayan mahaifin nata basu ji dadin ganinta sanye da Hijabin ba, inda suka ce zai fi idan ta tsaya a matsayinta ba sai ta nemi ta farantawa Musulmai rai ba ta hanyar yin abinda suke yi.

Wasu kuwa gani suke kawai ta mutunta wajen bauta ne, hakan ya sanya ta ga ya dace ta sanya Hijabi, ba wai don ta tozarta na ta addinin ko kuma karfafa guiwar a saka Hijabi ba.

KU KARANTA: Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu - Bincike

To sai dai kuma shi Allah ba a yi masa shishshigi a al'amuransa, idan ya so sai ya sanya mata kaunar addininsa, duk kuwa da irin kiyayyar da mahaifinta yake yiwa addinin na Musulunci.

A makon da ya gabata mun kawo muku labarin yadda wani fitaccen dan siyasa na kasar Netherlands, wanda aka bayyana cewa babu wanda ya kai shi tsanar addinin Musulunci a kasar ya Musulunta.

Mutumin mai suna Joram Van Klaveren ya Musulunta a daidai lokacin da yake rubuta littafin nuna kyama ga addinin Musulunci, bayan ya gama kiran Al-Qur'ani mai girma da cewa guba ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel