Tashin hankali: Watana shida ina karanta Bible, kuma ina samun kwanciyar hankali idan na karanta - Fatima Yusuf
- Yayin da kowa yake kokarin ganin yayi aiki tukuru ta hanyar karantar addinin Musulunci cike da waje ta hanyar amfani da Al-Qur'ani mai girma wajen nuna mana hanya
- Sai ga wata budurwa ta bayyana a dandalin sada zumunta na Twitter ta bayyana wani abu da ya bawa duk wani Musulmi Bahaushe mamaki
- Budurwar dai ta bayyana cewa ta shafe watanni shida tana koyar addinin Kiristanci a boye ba tare da kowa ya sani ba, sannan kuma tana jin dadi duk lokacin da ta karanta
Wata budurwa Musulma, mai suna Fatima Yusuf, ta bayyana cewa ta kwashe watanni shida tana nazari akan littafin Bible, kuma tana jin nutsuwa na shigar ta idan tana karantawa.
"Akwai wani abu na musamman game da shi, da yake kawo mini kwanciyar hankali da nutsuwa," ta rubuta a yayin da take bayyana irin jin dadi da kuma kwanciyar hankali da littafin yake bata a lokacin da take karantawa a boye.
Fatima ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter, ta ce ta shafe watanni shida tana karanta littafin Bible din a boye, kuma akwai wani abu na musamman a tattare dashi da yake bata nutsuwa, amma kuma ba ta san yadda za tayi bayaninsa ba.
Musulmai da yawa dai basa karanta littafin Bible, musamman iyaye wasu na hana 'ya'yansu kusantar duk wani abu da yake da bashi da alaka da Musulunci, domin kare 'ya'yansu daga komawa addinin da ba na Musulunci ba.
KU KARANTA: Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu - Bincike
Budurwar tana zuwa ta boye ne ta karanta littafin, inda ta bayyana hakan da take da abinda yake kawo mata jin dadi da nutsuwa.
To sai dai muce Allah ya kiyaye, ya kuma kiyaye mata imaninta, domin kuwa an ce idan kaga kare na shinshinar takalmi dauka zai yi, duk da dai budurwar ba ta bayyana cewa ta bar addinin Musulunci ba, to amma dai alamu na nuni da kadan ya rage ta canja hanya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng