Zazzabin 'Lassa': An kebe wasu mutane 70 a wata cibiya ta musamman a Kano
Kwamishinan lafiya a jihar Kano, Dakta Aminu Tsanyawa, ya ce an kebe wasu mutane 70 a wata cibiya ta musamman domin basu kula wa ta musamman bayan an yi zargin cewa sun kamu da zazzabin 'Lassa'.
Tsanyawa ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wata tattauna wa da manema labarai a wurin taron wayar da kai a kan zazzabin 'Lassa' a Kano.
Ya bayyana cewa an kebe wasu mutane 70 a wata cibiya ta musamman da gwamnatin jiha ta ware a Yar-Gayawa, yankin karamar hukumar Dawaki Kudu.
"Daga cikin mutane 390 da aka kebe sakamakon kamu wa da cutar, akwai mutane 70 da har yanzu suna kebe ana cigaba da duba lafiyarsu bayan an sallami wasu fiye da 300 da suka warke.
"Akwai mutane uku da aka tabbatar sun kamu da cutar kuma tuni aka sallame su bayan sun samu sauki.
"Gwamnatin jiha ta dauki matakan ganin cewa zazzabin 'Lassa' bai cigaba da yaduwa ba bayan ballewar annobar cutar a wasu jihohi da suka hada da Kano," a cewar Dakta Tsanyawa.
Dakta Tsanyawa ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakan kiyaye wa tare da samar da kayan aiki, musamman a filin jirgin sama, domin duba lafiyar duk wanda suka Najeriya ta jihar.
Ya bayyana cewa cibiyar da ke garin Yar-Gayawa ta dade ta kafa wa tare da bayyana cewa akwai kayan aiki a cibiyar da zasu kare likitoci daga kamu wa daga kamuwa da cutar.
DUBA WANNAN: Ibrahim Ibrahim: Dan Najeriya da aka yanke wa hukuncin kisa a kasar Saudiyya ya samu 'yanci
A cewarsa, akwai kayan aiki na zamani da dabarun duba lafiyar wadanda suka kamu da cutar, kuma an koya wa ma'aikatan lafiya a cibiyar yadda zasu kula wadanda suka kamu da cutar.
Dakta Tsanyawa ya kara da cewa gwamnatin jiha ta kirkiro taron wayar da kan jama'a a kan hanyoyn kare kai da dakile yaduwar cutar zazzabin 'Lassa', kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng