'Yan Hisbah sun damke mai maganin kara karfin mazakuta a Kano

'Yan Hisbah sun damke mai maganin kara karfin mazakuta a Kano

Jami’an hukumar Hisbah na jihar Kano sun damke wani matashi da ake zargi da sayar da maganain gargajiya na kara karfin maza. Hukumar ta zargi mutumin da amfani da kalaman batsa wajen tallata hajarsa.

Mataimakin shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano din mai kula da ayyuka na musamman, Malam Muhammad Albakari, ya shaida wa BBC cewa matashin na amfani da kalmomin batsa ne yayin tallata hajarsa. Munin kalaman ya kai ga sai an runtse ido idan har mutum zai saurara.

Matashin na tallar maganin ne a kasuwar Kofar Wambai da ke tsakiyar birnin Kano din. Yana kuma amfani da amsa-kuwwa wajen jawo hankulan jama’a zuwa ga maganinsa.

'Yan Hisbah sun damke mai maganain kara karfin mazakuta
'Yan Hisbah sun damke mai maganain kara karfin mazakuta
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Arewa na halaka kanta da kanta - Sarki Sanusi II

Hukumar ta Hisbah ta bayyana cewa, yanayin kalamansa da yake amfani dasu wajen tallata magungunansa basu dace ba.

Kamar yadda mataimakin shugaban hukumar ya bayyana, an damke saurayin ne bayan da aka kai musu koke a kan yadda yake amfani da kalaman batsa.

Muhammad Albakari ya ce ko bayan sun damke shi, sun kai shi ofishinsu ne inda suka yi masa wa’azi da jan hankali gami da nuna masa haramcin amfani da munanan kalaman batsan.

A cewarsa, sun kira iyayensa domin a yi masa nasiha a gabansu sannan suka sakesa tare da gindaya masa sharadin cewa, mataukar aka kara kama shi da irin wannan salon za a hukunta shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel