Hukumar EFCC ta ce dole a taso keyar tsohuwar Ministar Man fetur daga kasar waje

Hukumar EFCC ta ce dole a taso keyar tsohuwar Ministar Man fetur daga kasar waje

Shugaban hukumar EFCC na rikon kwarya, Ibrahim Magu, ya sake kira ga Birtaniya ta dawo da tsohuwar Ministan man Najeriya, Misis Diezani Alison-Madueke, gida.

Ibrahim Magu ya bayyana cewa hukumar EFCC ta gabatar da kara a kan Diezani Alison-Madueke, wanda ta tsere daga Najeriya tun kafin Shugaba Buhari ya hau kan mulki.

EFCC ta fara kokarin dawo da Alison-Madueke gida domin ayi mata shari’a tun 2018, amma lamarin ya gagara. Mista Ibrahim Magu ya ce su na gamuwa da kalubale.

Mukaddashin shugaban na EFCC ya yi wannan jawabi ne a wata hira da ya yi da ‘Yan jarida a Garin Kaduna. Magu ya ce Diezani Alison-Madueke ta saci kudin gwamnati.

Mista Magu ya ce abin da Misis Diezani Alison-Madueke ta sace a lokacin da ta ke rike da kujerar Ministan man mai a gwamnatin Najeriya ya kai akalla fam Dala biliyan 2.5.

KU KARANTA: EFCC: Tsohon Ministan shari'a ya zabi ya yi zamansa a cikin gidan yari

Hukumar EFCC ta ce dole a taso keyar tsohuwar Ministar Man fetur daga kasar waje
Abin da Diezani-Madukwe ta sace ya haura Biliyan 870 a kudin Najeriya
Asali: Depositphotos

“Ina Landan a shekarar nan, mun yi bincike da Tawagar Ingila, kuma duk inda na je, ina kiran a dawo mana da Barayin Najeriya su maido mana da dukiyarmu.” Inji Magu.

“Matar nan ta saci kudi sosai, abin da ya kai akalla Dala biliyan 2.5. Amma abin takaici an samu wasu gungun Barayi da su ke mara mata baya. Wannan ba abin kirki ba ne.”

“Mu na magana da kasashen ketare, ta na tsare a wani wuri ana kare ta, ba don haka ba, da mun kama ta, mun dawo da ita Najeriya. Ba za mu kyale rashin gaskiya a nan ba”

Mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC ya fadi irin hadarin rashin gaskiya, tare da bayyana cewa sun rufe asusu rututu wadanda ake zargin cewa akwai kudin sata a ciki.

Diezani Alison-Madueke ta rike Ministan mai na shekaru biyar a Najeriya, Kafin nan ta rike kujerar Ministan sufuri. Ana zarginta da satar makudan kudi daga dukiyar kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel