Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu - Bincike

Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu - Bincike

- Binciken da wata kungiyar taimakon kai da kai ta gida Najeriya ta gabatar ya nuna rashin shiga siyasar mata a Najeriya

- Rahoton ya bayyana cewa tun daga 1999, mata 36 ne kacal suka taba zama a majalisar wakilan Najeriya

- Sau da yawa a kan yi kalaman batanci da na nuna banbancin jinsi ga mata 'yan siyasa masu burin mulki

Wani rahoto daga kungiyar taimakon kai da kai mai suna Center for Information Technology and Development (CITAD) ta ce a tarihin majalisar dattijan Najeriya, mata 36 kadai suka taba samun zama sanatoci tun 1999, kamar yadda jaridar The Nation online ta ruwaito.

Rahoton CITAD din ya bayyana ne a wani taron horar da manema labarai da ta shirya a birnin Yola da ke jihar Adamawa. Kungiyar ta ce tun daga 1999 majalisar tarayyar ta samu mambobi 654 ne kuma gurbi 618 maza suka cike shi inda matan suka ciki 36.

Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu - Bincike
Mata 36 ne kawai suka yi mukamin Sanata a Najeriya tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu - Bincike
Asali: Facebook

An samu sanatocin 654 ne ta hanyar zabe tun bayan fara mulkin damokaradiyya a Najeriya. A kowanne lokacin zabe kuwa ana samun sanatoci 109 da ke wakiltar yankuna daban-daban na kasar nan.

Rahoton ya bayyana cewa, a cikin sanatoci 109 na 1999 an samu mata uku ne kacal. A 2003 an samu hudu, a 2007 an samu takwas, a 2011 an samu bakwai, a 2015 an samu 8 sai kuma 2019 an samu shida.

KU KARANTA: Matashi dan asalin jihar Kano ya fito da fasahar koyon addinin Musulunci a waya

A wani bincike mai zurfi kuwa, an gano cewa zai yuwu yawan sanatocin su gaza kai 36 saboda wasu matan ba sau daya suka lashe zabe ba. Misali ita ce Chief Remi Tinubu wacce ta ci zabe sau uku.

Hakazalika a bangaren mazan za a iya samun kasa da 618 don akwai sanatocin da ba karonsu na farko kenan a majalisar dattijan ba.

Rahoton CITAD din ya bayyana rashin shigar mata siyasa da kuma tsangwama da kalaman kiyayya da mata masu burin siyasa suke fuskanta.

Rahoton ya bayyana cewa, akwai kalaman kiyayya da kuma na nuna banbancin jinsi wanda ake wa mata masu burin siyasa. A kan kwantanta su da karuwai da sauransu. Hakan kuwa na taka rawar gani wajen cire burin siyasa daga zukatan mata kuma yana hana su cin zaben.

CITAD wanda ke da babban ofishi a jihar Kano ya horar da 'yan jaridu ne tare da hadin guiwa NDI da kuma shugaban hukumar, Hamza Ibrahim.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng