Hotuna: Dalibin makarantar sakandare a Najeriya ya kirkiri injin janareto da yake aiki babu fetir

Hotuna: Dalibin makarantar sakandare a Najeriya ya kirkiri injin janareto da yake aiki babu fetir

- A lokuta da dama dai akan samu mutane masu fasaha da basirar kirkirar abubuwa wadanda bamu da irinsu a Najeriya

- Amma matsalar rashin samun goyon baya na gwamnati ko kamfanoni ko kuma wasu masu hannu da shuni da irin wadannan mutane suke samu, sh yake sanyawa wannan basira ta su ta tashi a tutar babu

- Wannan takaitaccen labarin wani matashin saurayi ne dan makarantar sakandare da ya kirkiri fasahar wani injin janareto da yake aiki ba tare da an saka masa man fetir ba

Wani labari da yake ta faman yawo a kafafen sadarwa ya nuna yadda wani dalibin makarantar sakandare ta maza dake Aba, ya kirkiri wata fasaha da ta sanya mutane ake ta faman zancen shi.

Yaron wanda a lokacin da muke rubuta wannan rahoton ba a bayyana sunan shi ba, ya kirkiri injin janareto da yake aiki ba tare da man fetir ba.

Hotuna: Dalibin makarantar sakandare a Najeriya ya kirkiri injin janareto da yake aiki babu fetir
Hotuna: Dalibin makarantar sakandare a Najeriya ya kirkiri injin janareto da yake aiki babu fetir
Asali: Facebook

A wasu hotuna da suke ta faman yawo a shafukan sadarwa, an nuno yaron sanye da kayanshi na makaranta rike da injin janareton da ya kirkiri a hannunshi.

KU KARANTA: Jerin hanyoyi guda 7 da suka fi hatsari a Najeriya

Wani abin mamaki shine, za a ga cewa injin janareton bashi da nauyi kamar sauran injina irinshi.

Najeriya na cike da mutane masu fasaha ta ko ina amma rashin samun goyon baya ya sanya, wannan ilimi da fasaha da muke dashi yake tafiya a banza.

Mun kawo muku rahoton wani matashin saurayi dan asalin jihar Kano da ya kirkiri fasahar waya da za ta dinga taimakawa mutane suna karatun addinin Musulunci da suka hada da Hadisi, Figh da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng