Harin yan bindiga: Buhari ya tura manyan jami’an gwamnati zuwa jahar Katsina

Harin yan bindiga: Buhari ya tura manyan jami’an gwamnati zuwa jahar Katsina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawagar gwamnatin tarayya zuwa jahar Katsina domin ta jajanta ma gwamnan jahar Katsina, Sarkin Katsina da ma kafatanin al’ummar jahar Katsina bisa hare haren yan bindigan da suke fama da shi.

Premium Times ta ruwaito tawagar ta isa Katsina ne a ranar Litinin, 17 ga watan Feburairu a karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Abba Kyari, wanda Buhari ya umarcesu su samu masa cikakken bayani game da matsayin tsaro a jahar.

KU KARANTA: Za mu maka Buhari gaban kotu a kan wa’adin manyan hafsoshin tsaro – Falana

Cikin sakon taya alhini da Abba Kyari ya isar a Katsina, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa bisa mutuwar mutane 31 a harin da yan bindiga suka kai karamar hukumar Batsari, sa’annan ya jajanta ma iyalan mamatan.

Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka mutu, tare da fatan Allah Ya baiwa yan uwansu hakurin rashin da suka yi, sa’annan ya tabbatar ma masarautar Katsina da gwamnatin jahar Katsina cewa a shirye yake ya yi duk abinda ya kamata wajen kawo karshen ayyukan yan bindiga.

Gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda ya tarbi tawagar jim kadan bayan dawowarsa daga karamar hukumar Batsari inda ya kai ziyarar jaje, ya shaida ma tawagar cewa harin ya kawo cikas ga zaman lafiyan da aka samu a watanni 7 da suka gabata.

Sai dai yace babban abin da zai kawo karshen ayyukan yan bindiga shi ne samar da ingantaccen ilimi, don haka yace zai cigaba da baiwa ilimi fifiko a jahar Katsina, sa’annan ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Buhari bisa nuna damuwarsa da halin da suke ciki.

Shi ma a nasa jawabin, mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Kabir Usman ya gode ma shugaban kasa da ya tura wakilansa jahar Katsina don jajanta musu, don haka ya yi kira ga Sojoji da Yansanda su kara kaimi wajen yaki da yan bindiga.

Shuwagabannin Sojoji da Yansanda a jahar Katsina da suka halarci zaman sun gabatar da cikakken jawabi game da halin tsaro da ake ciki a Katsina, inda suka bayyana akwai jirgin sama mai gani da daddare wanda rundunar Sojan sama za ta yi amfani da shi don taimaka ma Sojojin kasa a yaki da yan bindiga.

Tawagar ta kunshi ministan tsaro, Bashir Magashi, ministan Yansanda Mohammed Dingyadi, ministan sufurin jirgin sama Hadi Sirika, shugaban hukumar leken asiri NIA, Rufai Ahmad, Garba Shehu da hadimin Buhari a kan harkan cikin gida, Sarki Abba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel