Jerin hanyoyi guda 7 da suka fi hatsari a Najeriya

Jerin hanyoyi guda 7 da suka fi hatsari a Najeriya

- A sannu kasar Najeriya ke zama kasar da ta fi kowacce miyagun tituna masu matukar hadarai

- Wasu titunan ba kwazazzabai bane kadai matsalarsu, fashi da makami da garkuwa da mutane ne yayi katutu

- Hukumar kiyaye hadurran kan titi ta kasa, FRSC ta bayyana cewa ana rasa rayuka 150,000 a kan titunan kasar nan duk shekara

A sannu kasar Najeriya ke neman cinye gasar kasar da ta fi kowacce miyagun tituna masu hatsarin gaske. Wannan kuwa ya dogara da yawan mutanen da ke mutuwa bane a kowacce rana a kan titunan. Kamar yadda hukumar kula da hadurran kan titi a Najeriya ta bayyana, sama da rayuka 150,000 ne ake rasawa a kowacce shekara a kasar nan sakamakon hadurran da suka danganci kan tituna. Abubuwan da ke kawo hadurran suna hada da: Cunkoson ababen hawa, fashi da makami, lalatattun tituna, lalatattun ababen hawa da sauransu.

Wasu daga cikin miyagun tituna a Najeriya sun hada da:

1.Titin Abuja-Lokoja-Okene-Kabba

Duk wanda ya taba tafiya a mota ta yankin Kudu maso yamma na kasar nan zai iya wucewa ta daya daga cikin titunan nan. Ba lalacewar kan hanyar kadai ba, kowa ya san yadda ‘yan fashi da makami suka yi katutu a kan wannan titin. Hakan ne kuwa ke haifar da hatsari mai yawan gaske.

2. Titin Legas-Sagamu-Ore-Benin

Wani mai kiyasi ya bayyana cewa, idan da akwai wani titi a Najeriya da ke nuna gazawar gwamnatocin da suka gabata na kasar nan, toh ba shakka wannan titin ne. Bayan lalacewarsa kuwa, manyan ‘yan fashi da makami na dankare a titin.

3. Babban titin Legas zuwa Ibadan

Anyi titin ne a 1974 mai tsawon kilomita 120. Titin ne kadai wanda ya hada Ibadan da jihar Legas tare da wasu jihohin yankin kudun. A 2012, an gano cewa an yi hadurra 2,075 kuma rayuka 775 aka rasa. Wannan hadurran na faruwa ne sakamakon kai da kawowar tankokin man fetur.

KU KARANTA: Tashin hankali: Kasar Koriya ta Arewa ta fara kashe mutanen dake dauke da Coronavirus

4. Titin Okigewa- Umuahia

Wannan ne babban titin jihar Enugu kuma ya kasance babban tarkon mutuwa a kasar nan. Bayan da ‘yan kwangila suka watsar da aikin gyaran shi saboda gwamnati ta ki sakin kudi, titin ya zamo tarkon mutuwa babba.

5. Titin Otukpo-Otukpa a Makurdi

Wannan titin na nan a jihar Benuwe ne kuma kwazazzabai da lalacewar titin ya kai inda ya kai. An gano cewa, ababen hawa na rawa a kan titin saboda lalacewar shi duk da kuwa babu kida.

6. Titin Enugu-Awka-Onitsha

Lalacewar wannan titin yasa wasu masu ababen hawan komawa tsohon titin Udu zuwa Awka. Wannan titin yayi sanadin rayuka da dama kuma har yau babban kalubale ne ga direbobi da kuma fasinjoji.

7. Titin Kaduna-Abuja

Wannan titin ya zama babbar mahada ga jihohi da yawa na arewa amma yana da kwazazzabai sama da 400. Bayan nan, fashi da makami da garkuwa da mutane yayi kamari a wannan titin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng