Yan Fim sun yi tir da shugaban hukumar tace fina fina game da yunkurin kama A Zango

Yan Fim sun yi tir da shugaban hukumar tace fina fina game da yunkurin kama A Zango

Barazanar da gwamnatin jahar Kano ta yi na kama fitaccen jarumin fina finan Kannywood Adam A Zango idan har ya shiga jagar Kano ya bar baya da kura, sakamakon zuwa yanzu abokan aikin Zango yan Fim sun yi tir da wannan barazana.

Shugaban hukumar tace fina finai na Kano, Malam Ismail Na’Abba Afakallahu ne ya tabbatar da wannan yunkuri na hukumarsa, inda yace za su kama Adam A Zango idan ya yi yunkurin yin wani taro a jahar Kano saboda ba shi da rajist da su a Kano, kuma yace ya fita daga Kannywood.

KU KARANTA: An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da mayakan Boko Haram a garin Maiduguri

Wannan barazana ya biyo bayan sanarwar da Zango ya fitar ne cikin wani bidiyo a shafin Instagram na Rahama Sadau, inda yake cewa zai shiga jahar Kano a ranakun Lahadi da Litinin don kallon sabon Fim din Rahama mai suna Mati A Zazzau, fim din da ya fito a matsayin Yarima a cikinsa.

Sai dai abin mamaki sai aka nemi Zango aka rasa a wajen shirin Fim din saboda wannan barazana ta kama shi. Amma a jawabinsa, Afakallau yace duk wanda ke ganin mutuncin Kanawa dole ne kuma ya bi dokokinsu, “Adamu baya son bin dokokinmu da tsare tsarenmu.” Inji shi.

Guda daga cikin jaruman fim da suka yi tir da wannan yunkuri shi ne Falalu Dorayi, inda yace kamata ya yi hukumar ta dinga dabbaka dokarta ba tare da nuna son kai ba, a cewarsa ba dole bane yin rajista da hukumar, dan fim zai iya fita idan har bai gamsu da tsare tsarenta ba.

“Idan har da hukumar za ta tantance fim, wanda kuma akwai jaruman da basu da rajista da ita a cikinsa, har ma ta amince a nuna fim din a gidajen kallo, toh banga dalilin da zasu hana wani dan fim mara jista mu’amala da masoyansa ba dan ya je kallon fim din.

“Idan har da gaske ne, kamata ya yi su soke fim din tun daga wajen tantancewa sakamakon akwai wadanda basu da rajista da ita a cikinsa, ko kuma su hana nuna fim din saboda haka. Na san yan fim da mawaka da dama da basu da rajist da hukumar amma kuma suna zuwa kallon fina finan da suka fito a cikinsu ba tare da an yi barazanar kamasu ba, toh me yasa ake ma Adam haka?” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng