Harin yan bindiga: Ministan sufuri Amaechi ya tsallake rijiya da baya a jahar Kaduna

Harin yan bindiga: Ministan sufuri Amaechi ya tsallake rijiya da baya a jahar Kaduna

Fasinjojin jirgin kasa da dama sun tsallake rijiya da baya yayin da wasu gungun miyagu yan bindiga suka kaddamar da farmaki a kan hanyar dake gab da tashar jirgin kasa dake tashi daga Kaduna zuwa Abuja, a unguwar Rigasa.

Daily Nigerian ta ruwaito lamarin ya faru ne da daren Lahadi, 16 ga watan Feburairu, kim kadan bayan jirgin ya sauke fasinjojinsa, inda yawancinsu suka kama sabuwar hanyar da ta tashi daga Rigasa zuwa Mando, daga cikinsu har da ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

KU KARANTA: Kamfanin NNPC ta kammala aikin daukan mutane 1050 aiki

Majiyar Legit.ng ta kara da cewa yan bindigan sun yi shirin kwantan bauna ne a kan titin na Mando sa nufin kai ma duk wanda ya bi hanyar farmaki, hangen ayarin motoci da suka yi kda wuya sai suka bude wuta, nan da nan Sojoji da Yansanda suka mayar musu da biki aka yi ta musayar wuta.

Guda daga cikin fasinjojin da harin ya rutsa dasu ya bayyana cewa: “Mun yi sa’a sosai cewa Yansanda Sojoji na kusa damu, har da ministan sufuri Amaechi a cikin fasinjojin, dan dole shi ma ministan ya koma kan hanyar Rigasa.” Inji Musa Lawan.

Da majiyar ta nemi jin ta bakin mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Kaduna, Mohammed Jalige game da lamarin, sai yace ba shi da masaniya, amma zai kara bincikawa.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan sama ta Najeriya ta bayyana rahoton dake yawo a kafafen sadarwa na cewa wai dakarunta sun kashe mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram guda 250, a matsayin labarun kanzon kurege.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wannan labari ya fara yawo a kafafen sadarwa ne tun a ranar 13 ga watan Feburairu, kuma wai ya fito ne daga wajen wani mutumi mai suna ‘Comr Aminu Shuaibu Musawa, kamar yadda hukumar sojan sama ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel