Jikar Dahiru Bauchi 'yar shekara uku ta haddace Qur'ani
Rukayyatu Fatahu Umar ta zamo daya cikin yara Musulmai kanana a duniya da suka haddace Al-Qur'ani mai girma. Jikar babban malami ce, Sheikh Dahiru Usman Bauchi daga diyarsa mai suna Sayyada Maimunatu Sheikh Dahiru Usman.
Karamar yarinyar ta fara haddar Qur'ani ne a wata makarantar Islamiyya da kakanta ya kafa. Makarantar kuwa na karkashin kular mahaifiyar yarinyar ne Sayyada Maimunatu.
Makarantar na nan ne a Bakin Ruwa a Kaduna.
Kamar yadda mahaifiyar yarinyar ta sanar, diyarta ta haddace littafin mai girma ne a lokacin da ta cika shekaru uku da watanni takwas a duniya.
Rukayyatu ta fara koyon karatun Qur'ani ne tun tana tsumman goyo saboda mahaifiyarta na da daliban da take koyarwa a dakinta.
Ta ce "muna amfani da dakina wajen karatu inda ake daukar darussan Qur'ani,"
"A lokacin, ina goyata a baya yayin da nake koyar da daliban. Daga nan ne ta fara bin daliban suna karatun. Babu dadewa kuwa ta fara haddace wasu surori," in ji Maimunatu.
DUBA WANNAN: Sauya su Buratai: Fadar shugaban kasa ta bankado shirin masu cin moriyar kungiyar Boko Haram
"Daga nan ne ta fara zama a aji inda ake hadda. A halin yanzu, ta kammala haddace Qur'ani. Ina matukar godiya ga mahaifina Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya dasa ni a wannan hanyar ta Musulunci," mahaifiyar ta ce.
Allah ya ci gaba da tsare mahaddaciyar. Ameen.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng